Cire Gwamna Fubara ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki — Lauyoyi
Shugaban ƙasa ba shi da ikon tsige zaɓaɓɓen gwamna bayan ayyana dokar-ta ɓaci a jiharsa.

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara
Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta soki matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na ayyana dokar ta ɓaci da kuma cire Gwamna Similanayi Fubara na Jihar Ribas.
Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, shugaban NBA, Mazi Afam Osigwe (SAN), ya ce a ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulki, shugaban ƙasar ba shi da ikon tsige zaɓaɓɓen gwamna bayan ayyana dokar-ta ɓaci a jiharsa.
- An shiga zaman ɗar-ɗar yayin da sojoji suka mamaye Gidan Gwamnatin Ribas
- Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau
“Saboda haka duk wani matakin da ya saɓa wa tsarin mulkin dimokuraɗiyya wanda kuma ya keta haddin cin gashin kan gwamnatocin jihohi,” in ji shi.
A kan haka ne Ƙungiyar Lauyoyin ta buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta yi watsi da duk wani yunƙuri na tsige Gwamnan Jihar Ribas da sauran zaɓaɓɓun jami’an da aka yi ba bisa ka’ida ba.
“Dole ne ya zamanto ayyana da dokar ta ɓaci ta dogara da ƙwararan dalilai na tsarin mulki, ba wai wata manufa ta siyasa ba.”
NBA ta yi gargaɗin cewa akwai barazana mai hatsarin gaske ta dakatar da zaɓaɓɓun jami’an da ke ƙarƙashin dokar ta ɓaci, wanda zai iya kawo wa dimokuraɗiyya cikas na buɗe ƙofar tsige zaɓaɓɓun gwamnatoci a nan gaba.
Kungiyar ta yi kiran cewa duk wani mataki da aka ɗauka a Jihar Ribas ya bi ka’idojin tsarin mulki da kuma ka’idojin dimokuraɗiyyar Nijeriya.
Kazalika, ta buƙaci duk masu ruwa da tsaki da suka haɗa da ɓangaren shari’a, da ƙungiyoyin farar hula, da ƙasashen duniya da su sanya ido sosai kan halin da ake ciki a Jihar Ribas domin daƙile duk wani yunƙuri da ke yi wa masu riƙe da madafun iko katsalandan ba bisa ka’ida ba.
Aminiya ta ruwaito cewa Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas bayan rikita-rikitar siyasa da jihar ta daɗe tana fama da shi tare da kuma da naɗa wanda zai riƙe muƙamin gwamnan jihar na tsawon wata shida.
Tinubu ya sanar da matakin ne a wani jawabi da ya yi ta kafafen talabijin na ƙasar da yammacin ranar Talata.
A cikin jawabin nasa, Tinubu ya yi nuni da yadda aka rushe ginin majalisar dokokin jihar watanni 18 da suka gabata, wadda aka kasa sake gina ta har zuwa wannan lokaci.
“Jihar ta tsaya cik tun bayan ɓarkewar rikicin siyasar inda aka tauye wa al’ummar jihar hakkinsu na cin moriyar mulkin dimokuraɗiyya.
“Na yi iyakar bakin kokarina wajen ganin yadda za a magance matsalar to amma duka ɓangarorin sun yi watsi da yunkurin.”
Tinubu ya ce “Bayan nazari kan halin da ake ciki a Jihar Ribas, ya zama wajibi na yi amfani da sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.
“A kan haka, na ayyana dokar ta-ɓaci daga yau 18 ga watan Maris, 2025.
“Da wannan bayani, gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu da kuma dukkanin zaɓaɓbun ’yan majalisar dokokin Jihar Ribas, an dakatar da su na wata shida, a matakin farko.
“A halin yanzu, na naɗa Vice Admiran Ibokette Ibas a matsayin wanda zai gudanar da lamurran jihar, domin amfanin al’ummar jihar,” in ji Tinubu.
Sai dai a cikin jawabin nasa, Tinubu ya bayyana cewa wannan doka da ya ƙaƙaba ba ta shafi ɓangaren shari’a na jihar ba.