Cire gwamnonin APC ko yaki da Arewa?
Edita don Allah ku ba ni dama na yi tsokaci dangane da abin kunyar da ‘yan majalisar Adamawa suka yi na tsige zababben gwamnansu, Hakika akwai kalubale wajen mutanen Arewa, ganin yadda ‘yan uba suka sako Arewacin kasar nan gaba ta kowane hali, sai sun mayar da Arewa baya. Kuma abin takaici sai ga shi […]
Edita don Allah ku ba ni dama na yi tsokaci dangane da abin kunyar da ‘yan majalisar Adamawa suka yi na tsige zababben gwamnansu, Hakika akwai kalubale wajen mutanen Arewa, ganin yadda ‘yan uba suka sako Arewacin kasar nan gaba ta kowane hali, sai sun mayar da Arewa baya. Kuma abin takaici sai ga shi ana amfani da wasu ‘yan Arewar, wadanda basa kishin Arewa. Ya kamata jama’ar Arewacin Najeriya mu hankalta, mu hada kanmu, mu daina yarda ana amfani da wasu domin cimma wasu bukatu..Daga Aminu Abdu Baka noma Sani Mainagge Kano 08099479880.
Allah Sarki dan Arewa
Allah sarki dan Arewacin Najeriya, wai yau har masifar takai ga duk wani dan Arewa mazaunin kudu, wai sai ya yi takardar shaidar zama dan kasa! Muddin yana da zama a wajen! Tambayata a nan shin wai Najeriya biyu ce? Sako daga faisal muh’d girei, a yola jahar adamawa,
Ba ma goyon bayan bashi
Mu talakawan Najeriya bamu goyon bayan Shugaba, Goodluck Jonathan akan bukatarsa na aro $1 biliyan domin yaki da kungiyar Boko Haram. Domin ba wani alfanun da kudin za su yi, kasancewar bai da zummar shawo kan wannan matsalar.Daga AbdulMalik Sa’idu Mai Biredi, Tashar Bagu Gusau.
Ta’aziyyar Rilwanu Lukman
Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un. Allah Ya jikan Dokta Rilwanu Lukman, Ya gafarta masa, ya yafe kura-kuransa. Daga kungiyar AMtasan Musulmi, YMC, Abuja. 08024929140.
Aminiya a kara adalci
Edita don Allah ka ba ni dama in yi tsokaci kan jaridar Aminiya. Jaridar Aminiya, jarida ce mai adalci da kyautata wa jama’a. Kirana ga wannan jarida shi ne ta kara adalci da hada kan al’umma da kyakkyawar fahimta. Daga Abubakar Barista Assada, Jihar Sakkwaton 09035600080.
Ga Gwamna Kwankwaso
Don Allah Aminiya ku mika min Jinjina ta musamman ga Gwamna Kwankwaso, saboda shi namijin duniya ne mai fadin gaskiya ko min dacinta. Allah Ya kare shi amin. Daga Nura Buhari Bondinga Lalas 07033155737.
Haba ’yan kadiriyya
Ku yi wa Shehu dahiru Bauchi adalci, ba ku fi shi son Shehu Usman danfodiyo ba. Daga Zakiru Abdullahi Mai Aski Fatakwal 08166908511.
Ga Murtala Nyako
Ka ga karshen maganganu marasa dadi. Ko Manzon (SAW) ya ce, “ku fadi alheri ko ku yi shiru. Magana mai dadi sadaka ce. Sai a kiyaye gaba. Ina yi maka fatan alheri. Allah Yasa haka shi ya fi zama alheri a gareka. Daga Mallam Lawal Shehu8 Daura 08064932628.
Ba amfani a dimokuradiyya
Wallahi ba mu ga amfanin dimokuradiyya a Najeriya ba. Daga Hassan da Hussaini Binanchi, Unguwar Magajin Garin Sakkwato da Baka Soyayya 08087436699.
Makomar dimokuradiyya
A fada wa Gwamnatin Najeriya, ta sani tsige gwamnonin ’yan adawa ba zai haifar wa kasar nan da mai ido ba. Daga Bashir S. Muhammad Gajida 07050364671.
Addu’ar ’yan matabn Chibok
Allah Sarki ’Yan matan Chibok, inda suka cika kwana 100 da sace su. Lallai wannan na iya gurgunta ilimi, musaman ga ’ya’ya mata. Muna addu’a albarkacin Ramadana Allah Ya kare al’ummarmu daga rikicin Boko Haram da sauran matsalolin tsaro da kasar nan ke fuskanta. Daga Salisu Hunukuyi, Sashen Nazarin Harsunan Afirka, Jami’ar ABU Zariya 08023666517.
Barka da sallah
Aminiya barka da aiki Edita ka ba ni da ma in mika sakon taya murna ga jama’ar Musulmi na duniya barka da sallah. Allah Ya nuna mana na badi muna raye. Amin ayi bikin sallah lafiya. Daga Alhaji Kankat Jihar Gombe 07085604839.
Ga ’yan wasan kwaikwayo
Assalamu alaikum Ma’aikatan Aminiya. Gaisuwa da jinjinawa zuwa gareku baki daya. Don Allah ku isar min da sakona. ’Yan dirama ba wa’azi suke yi ba; bata tarbiyya suke yi. Ku daina shiririta a duniya, ku koma kan gaskiya. Daga Hafsat Usman Bauchi 08109967691.
Jafaru Isa ne Gwamna a Kano
Edita ka ba ni dama in bai wa Kanawa shawara kan lallai su yi kokarin ganin an tsayar da Lawal Jafaru Isa takarar Gwamna a Kano. Domin daukacin ’yan siyasar da ke raba kudi da neman jan ra’ayin al’umma ban ga kamarsa ba.Daga kimar wannan gwarzo ta tabbata a lokacin da ya yi Gwamnan soja a Jihar Kaduna. Uwa-kaka barka, Lawal Jafaru Isa ya dau tuta a Kano. Allah Ya yi mana zabin alkhairi. Nura Muhammad kofar-Dawanau, Kano.
Addu’ar shugabannin Najeriya
Shugabannin Najeriya muna yi muku addu’ar bin kadin hakkinmu. Kuma da azuminmu a baki. Idan ku masu shiriya ne, Allah Ya shirya ku; idan kuwa ba masu shiriya ba ne, Allah Ya yi mana zabi mafi alkhairi, Ya karemu daga masu kulla makircin boye da na fili. Amin. Daga 08156575650.
Ta’aziyya ga Sarkin Hadeja
Edita don Allah ka mika min sakon ta’aziyata ga Sarkin Hadeja, bisa rasuwar danmasanin Hadeja, Dokta Lawan. Allah Ya yi masa rahama. Amin.Daga Ibrahim Sabo Iran Makwalla. 08052463475.
Alkibla sanin daidai sai Allah
Salam ra’ayina game da matsalar alkiblar masallatai. Muna da nisa da ka’aba, don haka zai yi wuya a ce wai lallai sai an samu saitin Ka’aba daga nan. Sanin daidai sai Allah, mu ’yan Adam. A daina kawo mana rudani; Musulunci na da sassauci. Allah ya taimaki Musulunci da Musulmi. Daga G.Y Majiya 08067742692.
Ga ’Yan Arewa
Edita, an fara tsige gwamnoni, ’yan Arewa sai a yi hattara. Allah Ya bai wa kasata Najeriya lafiya da zaman lafiya.Sako daga Garba Kyari karamar Hukumar Kafin Hausa, Jihar Jigawa. 08082297756.
Ga masu taimakon azumi
Jama’ar da suka taimaka wa al’umma da abinci, musamman a cikin wannan watan na azumi. Allah ka yi musu albarka, Ka albarkaci dukiyarsa. Allah Ka ba su aljnna Firdausi. Daga 07036054996.
Neman addu’a ga kasa
Ina so in una wa ’yan uwanmu Musulmi mu yi amfani da 10 karshen wannan wata mai albarka, mu dukufa da addu’ar neman zaman lafiya ga kasarmu. Daga Isah Ibrahim Gusau 08022583323.
Tsige Nyako kalubale ne
A gaskiya tsige Murtala Nyako wani kalubale ne ga siyasar Najeriya. Daga Nasiru Bello Gusau. 07068223562.