Cire tallafi: Kwanan nan farashin mai zai sauko – NNPC
Ya ce ‘yan Najeriya su daina fargaba
Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Mele Kyari, ya bukaci ’yan Najeriya su sha kuruminsu, saboda kwanan nan farashin man fetur zai sauka bayan cire tallafi.
Ya ce gasar da za a rika samu tsakanin manyan ’yan kasuwar mai zai sa tilas farashin man ya sauka, sabanin fargabar da ake da ita a yanzu ta tashin farashin.
- Alhazan Jigawa sun sake dawowa Kano bayan jirgin da aka canza musu ya samu matsala
- An kama mutum 3 sun yi wa ’yar shekara 12 fyade a Bauchi
Aminiya ta rawaito cewa a ’yan kwanakin nan dai layuka sun fara dawowa a gidajen man Najeriya sakamakon cire tallafin mai da kuma karin farashi.
A wata hirarsa da gidan talabijin na Arise ranar Alhamis, Mele Kyari ya ce janye tallafin zai haifar da sabbin ’ya kasuwa da zai sa man ya yi sauki sannan ya magance kakagidan da wasu ’yan kasuwar suka yi.
A cewarsa, “Amfanin cire tallafin shi ne za a sami sabbin ’yan kasuwa da za su shigo harkar wadanda a baya ba sa cikinta, kuma hakan zai sa abubuwa su yi sauki.”