…City ta fara zawarcin Coutinho

Kulob din Manchester City ya fara yunkurin dauke dan kwallon Liberpool Philippe Coutinho a karshen kakar wasa ta bana. Tuni kulob din ya taya dan kwallon a kan Fam miliyan 30 kwatankwacin Naira Biliyan bakwai da miliyan 440.Shi dai Courtinho dan kimanin shekara 22 a watan Fabrairun wannan shekara ce ya sabunta kwantaragin shekara biyar […]

…City ta fara zawarcin Coutinho
…City ta fara zawarcin Coutinho

Kulob din Manchester City ya fara yunkurin dauke dan kwallon Liberpool Philippe Coutinho a karshen kakar wasa ta bana.

Tuni kulob din ya taya dan kwallon a kan Fam miliyan 30 kwatankwacin Naira Biliyan bakwai da miliyan 440.
Shi dai Courtinho dan kimanin shekara 22 a watan Fabrairun wannan shekara ce ya sabunta kwantaragin shekara biyar a kulob din Liberpool amma City ta amince da duk sharuddan kwantaraginsa a Liberpool.
Kocin City Manuel Pellgrini ya ce kulob din ya fara yunkurin dauke dan kwallon ne ganin yadda dan kwallon tsakiyarsu Yaya Toure yake neman barin kulob din a karshen kakar wasa ta bana kuma Coutinho ne ake ganin zai maye gurbin Toure ba tare da wata matsala ba.
Coutinho dai ya taba buga wa kulob din Inter Milan na Italiya wasa kafin ya canza sheka zuwa na Liberpool kuma City ta amince ta rika biyansa albashin Fam dubu 150 kwatankwacin Naira miliyan 51 da dubu 150 a duk mako.