City ta kama hanyar lashe Firimiyar Ingila

A halin yanzu dai City ta bai wa Liverpool ratar maki 3 a teburin Firimiya.

City ta kama hanyar lashe Firimiyar Ingila

‘Yan wasan City yayin karawarsu da Newcastle United

Kungiyar Manchester City ta kama hanyar lashe gasar Firimiyar Ingila bayan ta lallasa Newcastle United da ci 5-0 a ranar Lahadin nan.

Wannan nasara da City ta samu ta kara mata karfin gwiwar lashe gasar ta bana la’akari da yadda Liverpool ta barar da damar ta ranar Asabar a karawar da ta yi da Tottenham wanda aka tashi 1-1.

’Yan wasan City zazzaga wa Newcastle United kwallaye 5 sun hada da Aymeric Laporte da Rodri da Phil Foden da kuma Raheem Sterling wanda ya jefa kwallon farko da ta karshe a wasan.

A halin yanzu dai City ta bai wa Liverpool ratar maki 3 a teburin Firimiya.

Yanzu haka Man City na da maki 86 a wasanni 35, yayin da Liverpoll ke da maki 83 a daidai lokacin da ya rage wasanni 3 a kammala gasar baki daya.

Chelsea na ci gaba da zama a matsayi na 3 da maki 67, yayin da Arsenal ke matsayi na 4 da maki 66, sai kuma Tottenham da maki 62 a matsayi na 5, Manchester United na matsayi na 6 da maki 58.