Ciwon Cibin-boko
Ciwon Cibin-boko shi ne babban abin da ya addabi Haurobiyawa, tun daga tsakiyar watan A-farin-lilo, har zuwa cikun Mayun dubu karamin lauje da sili da zagaye. Hakika wannan lamarin wafce tarin adon-gari har dari karamin lauje, al’amari da ya zamto ciwon uwa da uba; ciwon kasar Haurobiya. Domin ko a kundin labaran da ba mu […]
Ciwon Cibin-boko shi ne babban abin da ya addabi Haurobiyawa, tun daga tsakiyar watan A-farin-lilo, har zuwa cikun Mayun dubu karamin lauje da sili da zagaye. Hakika wannan lamarin wafce tarin adon-gari har dari karamin lauje, al’amari da ya zamto ciwon uwa da uba; ciwon kasar Haurobiya. Domin ko a kundin labaran da ba mu taba jin an iza keyar adon-gari masu tarijn yawa, an kuma jefa su cikin garari. Don haka makarantarmu ta Dodorido ke yunurin jefa azargagiyar zargi tasfka ta’asa a kan Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge da Uwargida Damo Hakuri da Shugaba Mai gudun-loko, musamman jin cewa sun nuna tababar aukuwar wannan lamari.
Ni dai Haurobiyawa ku taya ni dubi, wai ko balama da mariki da suran nau’ukan dabbbobin dawa da na gida har dari karamin lauje da doriya, aka cusa su cikin gingimarin shorido, ai sai an yi daga za a arce da su. A karatun wasikun jakin-dawa da na gida da na nutsa ina ta yi, ina ta yi, sai akwai na kakaba wa kaina tagiyar Malam Tambaya, shi yasa ma zan bijiro da tambayoyi: Wai wane namiji motsi gwamnatin Haurobiya ta yi a daidai lokacin da ta samu bayanai kan farmakin da aka kai a farfajiyar koyon watsattsake da buda wagagen littattafai ta sakan-ni-in-diren Adon gari da ke Cibin-boko, a Jihar Alan-guburo? Kodayake bai kamata in tuhumi mahukuntan Haurobiya kan zari rugar da aka yi wa adon gari a sakanni-in-dire ba, domin Shugabar iyayen giji ta jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, uwargida kima Cukwikuye, ta yi nuni da cewa a yi watsi da wannan lamari, tunda babu wanda ya baje namujiyarsa a daidai lokacin da aka tattara adon gari aka yi awon gaba da su.
Uwar gida Damo Hakuri, mai dakin Shugaban kasar Haurobiya, ita ma ta nuna tababarta kan samartakar berar da aka yi wa wadannan manyan jibi da gata a garin Cibbin-boko, amma da Uwar kungiyar Mabiya Addini da ke addu’a da gicciye a majami’un kasar Haurobiya suka baje sunayen ’ya’yanmu da suka bace, sai kuma labara ya sha bamban. Ganin haka uwar gida kima Cukwikuye, sai ta nemi masu watsatsake a mujallu da jaridu don ta lashe amanta. Ita kuwa uwargidan Shugaban kasar Haurobiya sai ta yi kukan zuki-ta-malle, domin wadanda suka yi arba da ita, sun tabbatar da cewa babu ko dison kwalla a kewayen namujiyarta. Duk da haka wadannan manyan sisi da kwabo ba su saduda ba, sai da suka sanya cincirindon iyayen giji da ke fafutikar ganin hukumomi sun yunkura wajen kwato ’ya’yan al’umma da aka yi awon gaba da su, wai an damke ja-gabar masu banga-banga.
Shagabannin Haurobiya mutane ne masu lasisin katobara da baranbarama. Kuma matsalar gama-garin al’umma da suke ja wa ragama, ba ita ce a gabansu ba. Farfajiyar koyon watsattsakensu daban, gidan Bokan-Turansu daban da na kowa. Don haka nike ganin Ciwon Cibin-boko matsala ce ta Haurobiyawa kawai, amma ba ta shagabanninsu ba.
A batu na waskiya, Shagabannin Haurobiyawa, musamman jiga-jigan Jam’iyya mai dan boto a snada jirge sun jefa azargagiyar zargi ga Gwamnan Jihar Alan-guburo da iyayen adon-gari, kan cewa su suka batar da ’ya’yansu, don kawai su bata sunan Gwamnatin Haurobiya, musamman a daidai lokacin da ake hankoron lashe zabi-sonka na shekara ta dubu karmain lauje da sili da baban lauje ke karatowa. Hasalima uwargida Damo hakuri, ta gaza yin na-damo, domin ta yi barazanar jan zuga, zuwa Jihar Alan-guburo don yin banga-banga da tsallen badake a kan titi, don tursasa Gwamna Gwaramgwam kan lallai ya fito da adon-garin da ya boye.
Babban lamarin da ya dugunzuma hankulan Haurobiyawa, shi ne, yadda iyayen giji suka yi gangami da cincirindon banga-banga a Haurubja da Ikko da sauran biranen kasar nan, amma har yanzu Gwmanatin Haurobiya sai alkawuran kanzon kurege take yi wa al’umma kan cewa za ta ceto adon-gari.
To, karshen tika-tika tik! An ce Uban-Mama zai taimaki Gwmanatin Haurobiya da tsuntsun sama mai layar zana, don kai farmaki Saman-bisa, inda ake tunanin an turke wadannan yara da ba su ji ba, ba su gani ba. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ita kanta kasar Uban-Mama ta nuna shakkun samunsu, domin akwai yiwuwar an arce da su zuwa Kamarun-Biya da kasar Chadi.
’Yan makaranta, ya kamata ku fasko cewa, shagabannin Haurobiyawa sun ki yin katabus ne saboda wanda aka yi wa diyarsa surar dan tsako da shaho ko shirwa ko hankaka ke yi wa kananan tsuntsaye. Uwa-uba an cusa wa gama-garin al’umma kiyayya da gaba, don rarraba kawuna bisa tafarkin kabaila-kabila da addini-adini.
Wai ina Samun-bom-da Sauki; ina Sufeto Mai taku da dan kulki; ina Barden Barade? Matukar wadannan jiga-jiga jami’an tsare dukiya da rayukan Haurobiyawa ba su labe a loko ba, to su yi wani namijin motsi don samun waraka daga Ciwon Cibin-boko.
Babbar mafita ga Haurobiyawa, mu dukufa wajen rokon Mai-duka ya yi mana agaji, sannan mu daina dora alhaki kowace irin ta’asa a kan masu haramta Bobo da kwambon bokoko. Mu dauka cewa wannan musifar ciwon ne da shafi mabiya da ke ibada a majami’a da masu fuskantar alkiblar kadaita Mahalicci da ibada, har ma wanda ba shi da wani abin bauta, matukar shin dan kasar Haurobiya ne. Ita kuwa hukuma, dole ne mu tursasata kan lallai ta nemi agajin makwaftanta, a hada karfi da karfe wajen laluben inda ’ya’yan al’umma suka shige. Kowane dan kasa nagari, lallai ya bayar da gudunmuwa wajen shawo kan wannnan musifa. Domin kada mu dauka cewa Amurkawa za su tsallako uwa duniya su agaza mana, ba tare da mun yi wani katabus ba. Rashin jajircewa kan wannan lamari, hakika ana iya sanyawa Ciwon Cibin-boko ya zama babban miki ga kasar Haurobiya, ko kuma mu ce an yanke wa furkaniyar yamutsa al’umma cibi, ta hanyar bobo da kwambon boko. Ni dai na roki Mai-duka ya kiyaye, ’yan makaranta ku amsa!