Ciwon daji na kashe mata 26 kullum a Najeriya —Zainab Bagudu
Matar Gwamnan Jihar Kebbi, Dokta Zainab Shinkafi Bagudu ta bayyana cewa mata 26 ne kullum ke mutuwa a Najeriya sakamakon ciwon daji na wuyan mahaifa wato Cervical Cancer. Dokta Bagudu ta ce Najeriya ta kere sauran kasashe a Afirka samun mata masu mutuwa a dalilin cutar ta sankarar mahaifa. Ambaliya: Mutum 15 sun mutu a […]
Matar Gwamnan Jihar Kebbi, Dokta Zainab Shinkafi Bagudu ta bayyana cewa mata 26 ne kullum ke mutuwa a Najeriya sakamakon ciwon daji na wuyan mahaifa wato Cervical Cancer.
Dokta Bagudu ta ce Najeriya ta kere sauran kasashe a Afirka samun mata masu mutuwa a dalilin cutar ta sankarar mahaifa.
- Ambaliya: Mutum 15 sun mutu a jihar Kebbi
- ‘kungiyarmu tana mara wa gwamnatin Yobe a yakar cutar shan-inna’
- Iska mai karfi ta rusa gidaje 300 a Kebbi
- Hatsarin jirgi ya rutsa da mata 10 a Kebbi
“Ina rokon iyayenmu musamman sarakuna da su taimaka mana wajen yaki da ciwon daji.
“Sama da mata miliyan 36.59 ne ke cikin hadarin kamuwa da cutar daji a duniya kuma mata 26 ne ke mutuwa kullum a Najeriya a dalilin ciwon”, cewar Dokta Bagudu.
Ta bayyana hakan ne a taron Ranar cutar Shan-inna ta Duniya da aka gudanar a Karamar Hukumar Argungun da ke Jihar Kebbi.
Cikin wani rahoto da BBC ta wallafa a bara, Dokta Zainab ta ce masana sun gano cewa cutar ta fi tsanani a Arewacin Najeriya saboda yawan haihuwa
Sobada haka ta yi kira da mata su rika takaita haihuwa ta hanyar rungumar tsarin ba da tazarar iyali.
A baya-bayan nan ne Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta cire Najeriya daga cikin kasashe masu fama da cutar shan-inna.