Ciwon Daji na kashe mutum dubu 700 duk shekara a Afirka —WHO
Akwai hasashen samun karuwar mace-macen zuwa kusan mutum miliyan daya duk shekara.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Gebreyesus
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce kusan mutum dubu 700 ke mutuwa sakamakon ciwon daji duk shekara a nahiyar Afirka.
Wannan dai a cewar WHO na faruwa ne yayin da a kowacce shekara a kan samu kusan mutum miliyan 1.1 da ke kamuwa da ciwon a nahiyar.
- Girgizar kasa ta yi ajalin fiye da mutum 240 a Turkiyya da Syria
- Musa Hasahya: Mutumin Uganda mai mata 12 da ’ya’ya 102 da jikoki 578
Daraktar Hukumar Mai Lura da Kasashen Afirka, Dokta Matshidiso Moeti, ce ta bayyana haka ranar Lahadi a wani jawabi da ta gabatar a bikin Ranar Yaki da Ciwon Daji ta Duniya mai taken ‘Inganta Hanyoyin Yaki da Cutar: Mu hada muryoyinmu domin daukar mataki’.
Ta ce hasashen da aka yi yanzu na nuna cewa akwai barazanar samun kashi 50 cikin dari na yaran da ake haihuwa da cutar a nahiyar Afirka zuwa shekarar 2050.
Ta kara da cewa, alkaluman sun nuna cewa akwai hasashen samun karuwar mace-mace sakamakon cutar kansa zuwa kusan miliyan daya a kowacce shekara zuwa 2030, idan ba a dauki matakan da suka dace ba.
Dokta Moeti ta ce kasashe 12 ne a nahiyar Afirka ke da kyakkyawan shirin yaki da cutar.
Jami’ar ta WHO ta ce Hukumar na taimaka wa kasashe 11 domin samar da ko inganta shirye-shiryensu na yaki da cutar.