Ciwon zuciya: Salman Khan zai dauki nauyin yi wa yara 100 aiki

Jarumi Salman Khan bai yi fina-finai masu yawa ba, amma a yanzu yana daya daga jaruman fina-finan Indiya masu yawan masoya. Ya tara masoya ne saboda saukin kansa da kuma iya mu’amala da jama’a. A yayin wani biki da aka kira ‘Eid’ ne jarumin ya bayyana cibiyarsa mai taimakon mutane mai suna ‘Being Human Foundation’ za […]

Ciwon zuciya: Salman Khan zai dauki nauyin yi wa yara 100 aiki
Ciwon zuciya: Salman Khan zai dauki nauyin yi wa yara 100 aiki

Jarumi Salman Khan bai yi fina-finai masu yawa ba, amma a yanzu yana daya daga jaruman fina-finan Indiya masu yawan masoya.
Ya tara masoya ne saboda saukin kansa da kuma iya mu’amala da jama’a.
 A yayin wani biki da aka kira ‘Eid’ ne jarumin ya bayyana cibiyarsa mai taimakon mutane mai suna ‘Being Human Foundation’ za ta dauki nauyin yi wa yara 100 masu fama da ciwon zuciya aiki.
Jarumin wanda kwanan nan ne ya fitar da wani sabon fim dinsa mai suna ‘Kick’, ya sanar a shafinsa na Twitter a ranar Talata cewa: “Barka da rana. Allah Ya ci gaba da kare mu daga dukkan masifu. Idan yaran da suke fama da ciwon zuciya kuma iyayensu ba za su iya daukar nauyin biyan kudin da za a yi musu aiki ba, to cibiyar Being Human Foundation za ta dauki nauyin biya wa yara 100 kudin aiki.”