Ciyaman ya naɗa hadimai kan harkokin doya da yalo a Enugu

Hadiman guda biyu za su kula da harkokin da suka shafi doya, yalo da kuma attaruhu.

Ciyaman ya naɗa hadimai kan harkokin doya da yalo a Enugu

Shugaban Ƙaramar Hukumar Igbo Etiti a Jihar Enugu, Eric Odo, ya naɗa Mataimaka Musamman guda biyu da za su ke kula da harkokin noma.

Na farko, Ezeugwu Frederick Ogbonna, zai kula da harkokin doya da barkono.

Na biyu, Nwodo Everestus Ugonna, zai mayar da hankali kan yalo da barkono.

Wannan na cikin takardun naɗin masu ɗauke da kwanan watan ranar 1 ga watan Nuwamba, wanda ya umarce su bayyana a ofishin ƙaramar hukumar da ke Ogbede don samun ƙarin bayani game da ayyukansu.

A cikin takardar naɗin Ezeugwu, an ce: “An naɗa ka a matsayin Mataimaki na Musamman na Shugaban Ƙaramar Hukuma kan Harkokin Noma (Doya da Barkono).

“Wannan naɗk ba aikin din-din-din ba ne face aikin gwamnati na wani lokaci, kuma yana ƙarƙashin ikon shugaban ƙaramar hukuma.”

Sanarwar ta ce ana sa ran waɗanda aka bai wa muƙaman za su gudanar da ayyukansu bisa tsarin gaskiya da amana.