Ciyar da dalibai ya jawo cinkoso a makarantun Kaduna
A ranar Litinin din makon jiya ne Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya kaddamar da shirin ciyar da daliban makarantun firamaren gwamnati abinci sau daya a rana. Wannan shiri na daya daga cikin alkawurran da Gwamnan ya yi a lokacin yakin neman zabe a bara. Kuma gwamnatin ta ce ta fito da tsarin ne […]

A ranar Litinin din makon jiya ne Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya kaddamar da shirin ciyar da daliban makarantun firamaren gwamnati abinci sau daya a rana. Wannan shiri na daya daga cikin alkawurran da Gwamnan ya yi a lokacin yakin neman zabe a bara. Kuma gwamnatin ta ce ta fito da tsarin ne domin janyo ra’ayin iyaye su rika tura ’ya’yansu a makaranta domin samun ilimi da rayuwa ingantacciya a nan gaba.
Gwamnan da wasu kwamishinoni da manyan jami’an gwamnatinsa ne suka kaddamar da shirin a Makarantar Firamare ta Titin Aliyu Makama a Unguwar Barnawa da ke fadar jihar.
Gwamna El-Rufa’i ya fadi wajen kaddamar da shirin cewa: “Wannan rana ce mai muhimmanci domin rana ce da ta nuna canjin da jama’a suka zaba. Daga yau gwamnatin Jihar Kaduna za ta rika ciyar da dalibai sama da miliyan daya da rabi. Aiki ne mai wuya, amma mun dauki alwashin aiwatarwa domin alkawari ne da muka dauka a lokacin yakin neman zabe.”
Gwamna Nasir El-Rufa’i ya ce, “Ciyar da daliban kalubale ne babba idan aka yi la’akari da girman aikin da kudin da za a kashe wajen samar da abincin a kullum, amma kuma ’ya’yanmu sun cancanci a yi musu fiye da haka. A yanzu haka aikin ciyarwar zai sama wa masu dafa abinci sama da dubu 17 aikin yi kuma kowacce a cikinsu za ta dauki ma’aikatanta da za su rika taimaka mata,” inji shi.
Ya yi kira ga masu dafa abincin su ji tsoron Allah wajen gudanar da aikin da aka ba su ta hanyar tsabtacewa da dafa abinci mai kyau ga daliban da ke karkashinsu domin a samu ingancin shirin.
Tun farko Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dokta Shehu Usman Adamu ya shaida wa jama’ar jihar cewa akwai wasu layukan waya na gaggawa da aka samar domin jama’a su kira su bayyana ra’ayinsu a kan wannan shiri na ciyarwa da kuma hanyoyin bi domin kara inganta shirin.
Aminiya ta gano cikin mako daya da kaddamar da shirin, ra’ayoyin jama’ar jihar ya karkasu a kan shirin, inda wasu ke ganin gwamnatin ta yi daidai wajen fito da shirin ciyarwar, wasu kuma na ganin ba ciyar da dalibai ba ne matsala, abin da ya kamata shi ne a gyara makarantu tare da samar da malamai isassu. A cewar masu wannan ra’ayi akasarin makarantun gwamnati babu kujerun zama, wasu babu ko allon rubutu.
Sannan akwai bayanan da ke cewa a wasu makarantun, dalibai na samun abinci yadda ya kamata a yayin da a wasu kuma ba su samun abincin a kan lokaci kuma bai wadata ba.
Akwai wasu iyayen da ke korafi a kan yadda ake bi wajen raba wa daliban abinci inda hakan ke jawo turareniya a yayin rabon, har a kai yaran suna samun raunuka.
Misali a ranar Juma’ar da ta gabata wasu dalibai sun samu raunuka sakamakon turereniya a Makarantar Firemare ta Layin Bilya da ke garin Rigasa lokacin rabon abincin. “Gaskiya abin akwai takaici domin kusan duk lokacin da aka zo raba musu abinci sai an yi turereniya saboda yawansu. Ina da ’ya’ya a makarantar, kuma a kan idona aka yi turareniyar, zan iya cewa babu tsari wajen rabon,” inji Malam Salisu Kano wani mazaunin Rigasa.
Ya ce tsarin da aka fitar na cewa kowane yaro ya kai kula ko robar karbar abinci na taimakawa wajen jawo turareniyar, tunda yaran layi suke yi suna karbar abincin kuma ga shi bai wadata. “A ganina ya dace a samu wadanda za su rika bi suna raba wa yaran abinci yadda ya kamata ba tare da sai yaran sun yi layi ba,” inji shi.
Ita kuwa Malama Hauwa Sulaiman daya daga cikin masu dafa abincin da take raba wa dalibai 470 a Makarantar Firemaren LEA ta Bakin Ruwa, Rigasa, ta bayyana wa Aminiya cewa a makarantar tasu doya da kwai take ciyar da yaran kuma komai na tafiya yadda ya kamata. “Muna da tsarin da muke bi wajen ciyar da yaran, an ba ni yara 470 ne kuma komai na tafiya cikin tsari. Muna bin umarnin da aka ba mu wajen yin abincin da raba shi. Sannan an ce mu da daina zuba wa yaran abinci a leda domin gudun yada cuta. Ba mu bai wa duk yaron da ya kawo leda abinci sai masu kula ko roba ,” inji ta.
Malama Hauwa ta yaba wa gwamnatin jihar saboda fito da tsarin ciyar da yaran, inda ta ce mata sun samu aikin yi maimakon zama babu sana’a.
Malama Fatima wadda ke dafa wa dalibai 398 abinci, ta ce tana raba faten wake ne a makarantar Firemare ta Badiko, kuma ta ce ba su da matsala a makarantar. “Ba mu samun wata matsala wajen dafa abinci ko raba shi ga yara a makarantarmu, sai dai wasunmu sukan dan samu tangarda wajen karbar kudinsu a mako a kan lokaci, amma muna fata za a magance matsalar. Baya ga wannan babu wata matsala da muke samu, kuma muna fata Allah Ya ci gaba da taimakon Gwamna a kan wannan aiki da ya sanya a gaba,” inji ta.
Ta ce ba su bai wa dalibai da suka kai leda abincin, domin an hana su. Sai ta roki iyaye su daure su saya wa ’ya’yansu kula ko robar zuba abinci.
Malam Mustapha Bulama mazaunin Unguwar Badarawa, Kaduna, ya ce gwamnatin jihar ta yi gaggawar kaddamar da shirin ciyar da daliban ba tare da la’akari da irin kalubalen da hakan zai janyo mata ba. “Ina ganin gwamnatin ta yi gaggawar kaddamar da tsarin ciyarwar ba tare da daukar ainihin kididdigar yawan daliban makarantu ba. Wannan ne ya janyo cinkoso har ta kai ga malamai ba sa iya koyar da daliban komai saboda yawan yara da aka dauka a makarantu.
“Akwai matsalolin da ya kamata a magance kafin so ma ciyar da yaran, misali gyara ajujuwa da samar da kujerun zama ga dalibai da malamai da samar da karin malaman da za su koyar. Wannan ya kamata gwamnati ta yi kafin kaddamar da ba da abincin,” inji shi.
Sai dai kuma Mustapha ya ce dole a yaba wa gwamnatin domin ta taimaka wajen fito da yaran da ba su zuwa makaranta wanda hakan zai taimaka a samu sahihin kididdigar yara marasa zuwa makaranta a jihar domin daukar matakin da ya dace.
Shugaban kungiyar Iyaye da Malamai na Makarantar UBE Primary School da ke Layin Bilya a Rigasa, Malam Idris M. Shariff ya ce daga lokacin da Gwamnan ya ce zai ba da ilimi kyauta makarantar ta cika ta batse da dalibai. Ya ce babban korafinsu shi ne karatu ba zai yiwu ba saboda cikar makarantar, kuma ajujuwa tara kacal suke da su. Ya ce a yanzu ajujuwan makarantar a cike suke da yara ga wasu a waje ma ake karantar da su domin abin ya zama matsala.
“Akwai gidan kaji kusa da makarantar kuma an yi magana da mai gidan kajin ya amince zai sayar wa gwamnati domin a fadada makarantar. An rubuta wa Kwamishinan Ilimi da Gwamna da duk inda ya kamata, domin a duba a sayi wurin a kara girman makarantar. Wannan ne makarantar gwamnati kadai a aunguwar kuma daliban Hayin Malam Bello da ’Yan Shanono da Titin Makarfi da Makera duk nan suke zuwa. Yaran nan a yanzu suna cikin halin matsi domin ba a koyar da su, kuma babu allunan da za a yi rubutu da su. A yanzu a jikin ajujuwa malaman ke rubutu, kuma da daliban sun ci abinci sai su tashi su tafi gida,” inji shi.
Game da zargin cewa yara na suma wajen rabon abinci, ya ce “A gaskiya ina makarantar nan da kaina na ga inda yara uku suka suma. Nakan bar ayyukana saboda taimaka wa wannan tsari na Gwamna. A da daliban makarantar nan dubu biyu da ne ’yan kai, amma yanzu sun kai dubu ashirin. Abin tambaya a nan shi ne wai a da duk yaran nan suna zaune ne a gida? Idan a gida suke zaune, ke nan nan da shekara goma zuwa sha biyar me yaran za su zama? Ashe ke nan Gwamna ya yi wani tunani da babu wanda ya yi shi, shi ya sa dole mu taimaka masa. Kawo yaran nan su yi karatu maimakon zama a gida suna yawo a bola da shan shalisho da sauransu dole a yaba wa Gwamna.
“Ina kira ga Gwamna ya zo ya ga makarantar Layin Bilya, sai ya zubar da kwalla idan ya ga yawan daliban. Ciyarwa da ya yi sadakatul jariya ce kuma kada ya damu da masu cewa bai yi daidai ba. Mu abin da ya yi dai-dai ne. Wannan kira da ya yi cewa dalibai su fito su yi karatu kyauta daidai ne. Domin a baya wasu ba su yi ba, sai dai cinye kudin gwamnati. Allah Ya saka masa da alheri shi ya sa muke taimakawa da karfinmu. Muna son ya zo ya ga makarantar Layin Bilya,” inji shi.
Wata Malama a makarantar da ta nemi a sakaya sunanta ta nemi gwamnati ta kara fadada makarantar da samar da ajujuwa domin dalibai su samu damar yin karatu cikin sauki. Ta ce babu alluna da bencina da kujerun zama. “Shi ya sa muke son gwamnatin nan ta taimaka mana da ajujuwa domin a dauke yaran nan daga cikin rana mu karantar da su ilimi yadda ya kamata,” inji ta.
Wakilinmu ya ziyarci makarantar firamare ta UBE da ke kauyen Unguwar Tata Bakin Kogi Garin Sarki Zubairu a karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna, inda ya tattauna da daya daga cikin shugabannin kungiyar iyaye da malamai mai suna Aminu Hayatu kan yadda ake tafiyar da ciyarwar. Aminu Hayatu ya ce “Mun yi na’am da yadda ake ciyar da ’ya’yanmu domin hakan yana sa wm yaran kwazon zuwa makaranta kuma a sanadiyyar ciyarwar kusan kullum muna samun karin dalibai masu bukatar su zo su yi karatu a makarantar.”
Sai dai shugaban ya koka cewa yaran da duke da su a halin yanzu ba a iya ciyar da su gaba daya, “Domin muna da dalibai 285 kuma wadanda ake iya ba abinci a kullum su 128 ne kawai. Kuma duk wanda ya kawo dansa ba a ba shi ba, to ba zai ji dadi ba, haka yaron da yake makaranta ya ga an ba dan uwansa ba a ba shi ba shi ma ba zai ji dadi ba. Dukkansu mabukata ne kamar yadda kake gane wa idanuwanka don haka muke roko a kauyaka irin namu gwamnati ta kara ba da himmar daukan dawainiyar ciyar da yaran gaba daya tunda adadinsu babu yawa. Yanzu haka da kake gani mukan yi dabara ne don haka kullum nake zuwa in sa ido in ga yadda ake yi, mukan fara ta kananan yara ne in mun ga sun samu to abin da ya rage sai mu raba wa sauran kadan-kadan domin su mai da yawunsu,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Ka san abinka da yaro dan wannan abin da aka ba shi na iya jawo hakalinsa wajen zuwa makaranta a koyaushe don haka muke shaida wa gwamnati wannan tsarin nata yana da kyau kuma ya kara karsashin zuwa makaranta don haka muna fatan Allah Ya sa mana hannu a wannan lamari domin ’ya’yanmu su samu ilimi mai amfani. Idan ka lura za ka ga kusan duk daliban kayan da ke jikinsu na gida ne ko kakin da za su sa na makaranta ya gagara a dinka musu domin matsanancin talauci da iyaye ke fama da shi don haka ciyarwar nan ta taimaka kwarai da gaske.”
daya daga cikin masu dafa abincin mai suna Zaituna ta ce, “An ba ni ciyar da yara 128 ne kuma faten wake nake dafawa in kawo kamar yadda ka gani yanzu. Na zo da shi kuma an ba ni wannan aiki ne a kan Naira dubu shida da 400 kuma an ba ni ranar daya ce wato ranar Laraba a mako kuma alhamdullilahi mun gode saboda ’ya’yanmu ne ake ciyarwa kuma ni ’yar wannan unguwa ce don haka zan yi iya kokarina in ba da tawa gudunmawar, dan abin da na samu in hakura da shi domin in ban samu ba yau to zan samu gobe.”
Haka kuma wakilin Aminiya ya ji ta bakin daya daga cikin yaran da ya karbi nasa abincin mai suna Salmanu Sani mai shekara takwas kuma yake aji biyu, ya ce yana jin dadin abincin da ake ba shi kuma ya gode.
Sai dai wakilinmu ya lura cewa duk yaran da suke karatu a makarantar babu mai yunifom a jikinsa kuma dukkansu suna zaune a kasa ne kuma ajujuwansu kanana ne, inda ake hada yaran aji shida da aji biyar a aji daya. Ya ce idan za a karantar da ’yan aji shida sai ’yan aji biyar su juya baya, bayan an kammala karantar da su, sai su kuma su juya baya yan aji biyar su juyo su ma a karantar da su. A cewar wakilinmu haka ma ake hada ’yan aji hudu da uku a aji daya kamar yadda aka yi wa na gaba da su su ma haka ake yi musu, haka ’yan aji biyu da aji daya suna cakude ne a aji daya saboda karancin ajujuwa da suke fama da su ga kuma yawan dalibai.
Wakilinmu namu ya gano ajujuwan babu silin babu tagogi haka kuma babu kofofi haka dai makarantar ta kasance sai dai tana da malamai masu karantarwa guda tara.
daya daga cikin malaman da ya nemi a sakaye sunansa ya yi kira ga gwamnati ta sanya makarantarsu a cikin makarantun da za a gyara da kuma kara yawan ajujuwa. Ya ce tun daga lokacin da aka fara ciyar da dalibai a makarantar kusan kullum sai an kawo yara, kuma babu inda za su sanya su sai dai su ba iyaye hakuri har sai in an samu karin ajujuwa, to za su dauka zuwa nan gaba.