Ciyo wa Najeriya bashi zalunci ne da bautar da na baya —Sheikh Nuru Khalid

Allah Ya wadata Najeriya da hanyoyin kudin shiga da ba sai ta ciyo bashi ba.

Ciyo wa Najeriya bashi zalunci ne da bautar da na baya —Sheikh Nuru Khalid

A makon jiya ne aka samu labarin cewa Gwamnatin Tarayya za ta kara ciwo wani sabon bashi domin gudanar da ayyyuka a kasar nan, lamarin da ya tayar da kura musamman a kafafen sadarwa, har ta kai  mutane suna kiyasta kudin da ake bin kowane dan Najeriya.

Wannan ya sa wadansu suka fara tambayar, yaya matsayin bashin yake a kan dan kasa.

Hakan ya sa Aminiya ta nemi jin ta bakin malaman addini domin sanin yadda lamarin yake.

Da yake amsa tambayoyin Aminiya kan lamarin, Babban Limamin Unguwar ’Yan Majalisar Dokoki ta Kasa da ke Abuja, Sheikh Nuru Khalid, ya soki cin bashi da shugabanni a matakan gwamnatoci uku suke yi da sunan yin ayyukan raya kasa ko tallafa wa rayuwar al’umma, inda ya bayyana lamarin a matsayin zalunci.

Sheikh Nuru Khalid wanda ya zanta da Aminiya, ya ce larurorin da suke sa a ciyo bashi a Musulunce sun hada da matsalar yunwa a tsakanin al’umma da annoba ko rashin nagartattun cibiyoyin kiwon lafiya da na ilimi da kuma samar da tsaro.

“Haka kuma za a iya ciyo bashi don yin aiki kamar na gyaran hanyoyi idan ana rasa rayuka a dalilin muninsu,” inji malamin.

Sai dai ya ce, Allah Ya wadata Najeriya da hanyoyin kudin shiga da za ta iya magance mataslolin gaba daya ba tare da ta ciyo bashi ba, kamar yadda ya ce masana a harkar kudi suka yi ittifaki a kai.

Ya ce, matsalar kasar nan ita ce almubazzaranci daga bangaren wadanda suke rike da dukiyar kasar, inda suke sayen motoci da gidajen alfarma da yadda suke gudanar da bukukuwa a tsakaninsu.

Malamin ya ce Najeriya ba ta da matsalar talauci sai kawai matsalar kekashewar zukatan shugabanninta da ma’aikata da suke almubazzaranci da dukiyar al’umma da Allah Ya damka musu.

“Munin bashi ya sa har Manzon Allah (SAW) yana kin yin Sallah ga mamaci matukar ya mutu dauke da bashi a kansa.

“Sannan saboda nauyin bashi Musulunci ya yarda a dauki dukiyar zakka a biya wa mai bashin.

“Ba daidai ba ne mutum ya ciyo bashin da ba zai iya biya ba, sai dai ya ce ’ya’yansa ko jikokinsa ne za su biya, saboda yin hakan tamkar ya jinginar da su ne kuma zalunci ne kasancewar idan suka gaza biya, za a bautar da su,” inji malamin.

Limamin ya bayyana irin bashin da gwamnatocin kasar nan suke ci a yanzu wanda yawanci wa’adin biyan na kai har bayan sun sauka daga mulki, a matsayin jinginar da al’ummarsu a tsarin siyasar duniya, wanda ya ce ba ya taimaka wa wanda ya ci bashin sai dai mai bayarwa.

“A Musulunce matukar ba a kan larura shugaba ya ciwo bashi ba, to lallai ya zalunci al’ummarsa a tsarin siyasar duniya, sannan idan an je Lahira kuma laifin a kansa yake, ba al’ummar ba.

“Lokacin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya zagaya duniya yana faduwa kasa tare da neman a yafe wa kasar nan bashi, saboda illarsa da yadda ya zama ala-kakai, ya kamata mu dauki darasi a kai, amma ba mu dauka ba.

“Hanya guda da shugabanni za su wanke kansu, ita ce su nemi jin ra’ayin ’yan kasa kafin su ciyo bashin.

“Kuma hujjar cewa ana gabatar da bukatar haka a gaban wakilan majalisa ba dalili ba ne, saboda kowa ya san ba hakikanin jama’a suke wakilta ba illa kansu,” inji shi.

– Abin akwai tashin hankali — Archbishop Kaigama

Shi kuwa Shugaban Darikar Katolika a Najeriya, Akibishop Ignatius Kaigama, Kuma Akibishop din Katolika na Abuja, ya shaida wa Aminiya cewa basussukan da ake ciyowa a Najeriya, abin tashin hankali ne.

Ya ce, “Gaskiya idan mutum yana da matsala, addinin Kirista, bai hana ya je ya nemi taimako ba, domin cin bashi neman taimako ne.

“Amma a nemi taimako, a wajen da zai yi amfani, wanda zai fitar da mutum daga cikin matsalar da yake ciki.”

Akibishop Kaigama, ya ce, “Cin bashin da Najeriya take yi, na kudade masu yawa daga kasashen waje, don a zo a yi ayyuka a Najeriya, abin yana tayar mana da hankali.

“Domin ana ta ciyo bashi, amma ba mu ga abin da ake yi a fili ba, wanda zai nuna wannan bashi da suke ciyowa.”

Ya ce a shekarun baya, basussukan da Najeriya ta ciyo sun yi yawa har gwamnati ta yi kuka aka yafe mata. Yanzu kuma an koma gidan jiya ana ta ciyo bashin.

Ya ce, “Ana ta ciyo basussuka, kamar hayaki ba tare da ganin abubuwan da ake yi ba.

“Ba a hana karbar basussuka ba, amma me ake yi da su? Don haka, muna fatar idan za a ci gaba da ciyo basussukan nan, a ciyo da tsoron Allah.

“Idan da ana ciyo basussukan nan, a yi ayyukan asibitoci da makarantu, za mu gode musu.”

Don haka, ya yi kira da a yi hankali da basussukan da ake ciyowa, “Kada mu karbo abubuwa da za su kawo wa yara na baya damuwa sosai, a lokacin da ba ma nan,” inji shi.

Ya ce a yi hankali da wadannan basussuka, domin ba mai son a rika bin sa bashi.

“Mu yi tunani kan kudaden da muke kashewa wajen tafiyar da gwamnati, kamar a Fadar Shugaban Kasa da fadojin gwamnatocin jihohi da ’yan majalisa da sauransu.

“Mu tsaya a kan yaki da cin-hanci da rashawar nan, idan muka yi haka, za mu samu kudaden da za mu yi aiki da su,” inji shi.

– ‘Zaben 2023 na ban tsoro’

Da ya juya kan zaben 2023 da ake tunkarowa, Akibishoo Kaigama ya ce, “Na ga irin marmarin da ’yan siyasa suke da shi a kan zaben shekarar 2023, tun shekarar ba ta zo ba.

“Yanzu hankalin ’yan siyasa yana firgice kowa ya rude. Kowa yana neman matsayin da zai samu a shekarar 2023.

“Ya kamata mu sani cewa shekarar 2023, Allah ne kadai Ya san abin da zai yi a kai.

“Gaskiya hankalina yana tashi, kan wannan lamari, domin ina ganin nan da ’yan watanni, kila ba za a gane kan masu mulki a kasar nan.

“Kowa ya damu kan abin da zai faru da shi a zaben 2023. Wannan ba siyasa ba ce, siyasa ita ce a taimaki jama’a.”

Bishop Kaigama ya ce, “Muna cikin mawuyacin hali a Najeriya, a kowane bangare, ta fannin kiwon lafiya ne, ta bangaren tsaro ne, ta bangaren tsadar abinci ne, duk muna cikin mawuyacin hali.

Amma duk da haka, mu ci gaba da addu’a Allah Ya taimaki musu mulki, Ya ba su hikima kan yadda za su taimaki talakawa da mutanen Najeriya, baki daya.

Mu kwantar da hankalinmu, mu guji saba wa juna saboda addini ko kabilanci ko yanki, wannan ba zai taimake mu ba.”