Cizon Kare Ya Tashi Hankalin Mazauna Nasarawa

An yi kiran masu karnuka da su dauki matakin ɗauresu a lokacin da jama’a ke zirga-zirga.

Cizon Kare Ya Tashi Hankalin Mazauna Nasarawa

An samu tashin hankali a Yammacin ranar Alhamis a Unguwar Sabuwar Madina, da ke Juwape Phase 2 ta Marabar Gurku a Jihar Nasarawa, bayan wasu karnuka sun cicciji wani magidanci da ya je sallar Asham.

Abdul Zuru ya gamu da wannan jarrabawar ce bayan ya fito daga masallaci yayin da ake raka’o’in karshe a sallar Asham.

Ya bayyana wa Aminiya cewa, “an idar da tarawihi lokacin za a yi shafa’i da witiri sai na fito tare da dana domin mu tafi gida, sakamakon bana jin dadin jikina.

“Muna fitowa akan kwana sai karnukan suka far mana, in da Allah Ya taimakeni na kubutar da dana, ni kuma suka ciccijeni a cinya”.

Daga nan ne hankalin jama’a ya kai gare su inda aka kai masa dauki nan take kuma aka garzaya dashi asibiti domin neman magani.

Karnukan dai mallakin wani makwabcin Abdul ɗin ne da ake kira da Abdurrazaq Rasko.

Faruwar hakan ce ta sa iyalan Rasko suka buga masa waya, suka kuma sanar da shi cewa karnukansa sun ciji wani makwabcinsa, inda ya zo da gaggawa.

Da zuwansa ya samu jama’ar anguwar cikin tashin hankali da sanduna suna cewa a fito musu da karnukan su kashe su kawai.

Da kyar shugaban kwamitin Unguwar, Injiniya Lawal Abbas ya kwantar wa jama’a hankali suka hakura, aka kuma bai wa Rasko umarnin ya fitar da karnukan daga anguwar cikin gaggawa.

Kazalika, an rubuta takardar yarjejeniya kan cewa Rasko zai fitar da karnukan daga anguwar.

Mai Unguwar Sabuwar Madina, Malam Lawal Muhammad, ya yi kira ga duk masu karnuka a Unguwar da su dauki matakin ɗauresu a lokacin da jama’a ke zirga-zirga.

Ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan kura ta lafa kuma hankalin jama’a ya kwanta.

Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala —Uba Sani

Yau Majalisar za ta ci gaba da aiki kan Dokar Haraji

Kotu ta tsige Ohinoyi na Ƙasar Ebira

Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano