Club Brugge ya taya dan kwallon Super Eagles Naira biliyan 2
Rahoton da jaridar labaran wasanni ta Complete Sport ta kalato ya nuna kulob din Club Brugge da ke Beljiyam ya taya dan kwallon Super Eagles, Paul Onuachu a kan Yuro miliyan 5 (kimanin Naira biliyan 2). Paul wanda yana daya daga cikin ’yan kwallon da suka yi wa Najeriya kwallo a Gasar Cin Kofin Afirka […]
Rahoton da jaridar labaran wasanni ta Complete Sport ta kalato ya nuna kulob din Club Brugge da ke Beljiyam ya taya dan kwallon Super Eagles, Paul Onuachu a kan Yuro miliyan 5 (kimanin Naira biliyan 2). Paul wanda yana daya daga cikin ’yan kwallon da suka yi wa Najeriya kwallo a Gasar Cin Kofin Afirka da aka kammala kwanan nan a Masar yana yin kwallo ne a kulob din Midytlland da ke Denmark kuma a kakar wasan da ta wuce ya zura kwallaye 14 a raga cikin wasanni 39 da ya yi wa kulob din. Idan cinikin ya kaya, Paul zai zama daya daga cikin ’yan kwallon Najeriya da kulob din Club Brugge ya saya a bana.
Tsohon dan kwallon Eagles Daniel Amokachi ya taba yi wa Club Brugge kwallo.