Coci mai siffar tsinin takalmin mata ya bayyana Taiwan
Wani abin mamaki ya bayyana a kasar Taiwan, inda aka gina wani Coci mai siffar takalmin mata mai tsinin duga-dugi. Wannan cocin zamani an gina shi ne a Kudancin gabar kogin Taiwan. Kuma tsawon sa da fadin sa sun kai mita 17 da 11, sannan an kawata su da gilashi har guda 320.A cewar jami’in […]
Wani abin mamaki ya bayyana a kasar Taiwan, inda aka gina wani Coci mai siffar takalmin mata mai tsinin duga-dugi. Wannan cocin zamani an gina shi ne a Kudancin gabar kogin Taiwan. Kuma tsawon sa da fadin sa sun kai mita 17 da 11, sannan an kawata su da gilashi har guda 320.
A cewar jami’in mulki na wannan yanki mai kawatarta, wannan Coci an yi masa gini mai ban sha’awa, amma a hakikanin gaskiya an cakuda tsarin al’adu ne a wajen ginin. Domin a al’adance, amarya na sanya takalmi mai tsini, don yin taku a kan duwatsun alfarma na daben daki, sannan ta watsar da su don shiga cikin ’yan uwan iyalan ango, al’amarin da ke nuni da kawo karshen musifun da suka gabata, da kuma share fagen samun kyakkyawar rayuwa. Saboda haka an gina wannan coci ne mai siffar takalmin mata mai tsini don daura auren angoi da amarya da kuma daukar hotuna.
An sa ran bude wannan Coci a cikin watan Fabrairun wannan shekarar, lokacin bikin bazaar na shekara-shekara.