Cocin Katolika ya tallafa wa mutanen kauyen Kizara

Cocin Katolika na Our Lady of Fatima da ke Jihar Zamfara a karkashin jagorancin Bishop din Sakkwato Bishop Mathew Kuka ya tallafa wa jama’ar kauyen Kizara da kayan abinci da suka hada da shinkafa da masara da dawa da gero da kuma tufafi da aka yi kiyasin sun kai na sama da Narai miliyan biyu […]

Cocin Katolika ya tallafa wa mutanen kauyen Kizara
Cocin Katolika ya tallafa wa mutanen kauyen Kizara

Cocin Katolika na Our Lady of Fatima da ke Jihar Zamfara a karkashin jagorancin Bishop din Sakkwato Bishop Mathew Kuka ya tallafa wa jama’ar kauyen Kizara da kayan abinci da suka hada da shinkafa da masara da dawa da gero da kuma tufafi da aka yi kiyasin sun kai na sama da Narai miliyan biyu da kuma tsabar kudi Naira dubu 250.
Da yake gabatar da jawabi a wurin ba da tallafin Bishop Matthew Kuka ya ce sun kowo tallafi ne don su nuna tausayawarsu ga jama’ar Kizara, sakamakon halin da suka tsinci kansu a ciki na jarrabawa.
Ya ce sun yi haka ne don nuna tausayawa da nuna suna tare da jama’ar kizara, duk da cewa babu Kiristan da ke zaune a kauyen, “Kuma mun zo da kananan yaranmu ’yan makaranta wadanda za su yi hadu da yaran garin don tausayawa.”
Mai martaba ’Yandoton Tsafe Alhaji Habib Aliyu ne ya karbi kayayyakin, inda a jawabinsa ya nuna matukar farin ciki da godiyrsa ga cocin, kuma ya ce wannan ya nuna yadda Kiristoci da Musulmi suke zaune lafiya a Jihar Zamfara, inda ya nemi sauran Kiristocin kasar nan su rika koyi da irin wannan kokari da cocin ke yi.