Coge a kasafin kudi: Yau Dogara zai bayyana inda ya dogara
Yau ne ake sa ran Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara zai bayyana inda ya dogara kan zargin da ake yi masa shi da Mataimakinsa Yusuff Lasun da Babban Mai tsawatarwa na Majalisar Alhassan Ado Doguwa da Shugaban Marasa Rinjaye Leo Ogor kan yi coge a kasafin kudin bana. Shugabannin majalisar za su bayyana a gaban […]
Yau ne ake sa ran Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara zai bayyana inda ya dogara kan zargin da ake yi masa shi da Mataimakinsa Yusuff Lasun da Babban Mai tsawatarwa na Majalisar Alhassan Ado Doguwa da Shugaban Marasa Rinjaye Leo Ogor kan yi coge a kasafin kudin bana. Shugabannin majalisar za su bayyana a gaban wani kwamitin bincike na ’yan sanda ne mai mutum biyar da Mukaddashin Sufeto Janar Ibrahim Idris ya kafa domin bincikar zargin da ake yi musu.
Kwamitin ya yi ganawar sharar fage da tsohon Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Abdulmumini Jibrin wanda ya zargi su Dogara da yin cogen Naira biliyan 384 a cikin kasafin.
A ranar Litinin da ta gabata ce Abdulmumini Jibrin ya rubuta takardar korafi ga ‘’yan sanda da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na FECC da ICPC kan lamarin. Kuma ana jin ya yi ba kwamitin ’yan sandan wasu muhimman bayanai da dimbin takardu a ganawarsu ta ranar Talata.
Wata majiyar ’yan sandan ta ce, Shugaban ’Yan sandan ya umarci kwamitin ya gudanar da binciken kwakwaf kan takardar koken ta Jibrin.
Kwamitin yana karkashin wani kwararren mai bincike Mataimakin Sufeto Janar Amodu Ali, wanda shi ne ya binciki badakalar cin hanci ta Dala dubu 620 da ake zargin tsohon dan majalisa Farouk Lawan da karba daga fitaccen dan kasuwar nan Femi Otedola wanda yanzu ake gaban kotu.
Jam’iyyar APC ma ta gana da bangarorin biyu na Dogara da Jibrin domin magance takaddamar.
Wata majiya ta ce Dogara ne ya fara ganawa da uwar jam’iyyar kafin Jibrin.
Sai dai majiyar ta ce a ganawarsa da jam’iyyar Jibrin ya bukaci ta tilasta Dogara ya kira zaman majalisar domin ya koma gefe don fuskantar zargin coge a kasafain kudin na bana.
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC ta kasa, Sanata Lawan Shu’aibu ne ya kira ganawar, inda ya ce manufarta a kawo karshen takaddamar Jibrin da shugabannin majalisar.
A wani zargi na baya-bayan nan Jibrin ya zargi Yakubu Dogara da bayar da cin hanci Dala dubu 25 ga wadansu zababbun ’yan Majalisar Wakilai domin su kada masa kuri’ar goyon baya. Ya yi zargin cewa wadanda aka ba alhakin tsara tattara sanya hannun nuna goyon bayan su ne Honorabul Zakari Mohammed da Jagaba Adams Jagaba da kuma mataimakin shugaban ma’aikata na Shugaban Majalisar Honorabul CID Maduabum.
Sai dai nan take Zakari Mohammed ya musanta zargin inda ya bayyana shi da tatsunniya.
in a tweet kuickly debunked the allegation. “Ina son in bayyana wannan zargi ba ma karya ba ce kawai, har ma wata tatsunniya ce da aka shirya don zubar min da mutunci a idon ’yan Najeriya,” inji Zakari.