COJOYA da Jama’atu sun shirya bita game da gwaji kafin aure

Kungiyar ci gaban matasa da ake kira COJOYA da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato, tare da hadin gwiwar Kungiyar Jama’atu Nasril Islam, reshen Karamar Hukumar Jos ta Arewa, sun shirya wani taron wayar da kan al’ummar Musulmi kan muhimmancin yin gwaje-gwajen cututtuka kafin a daura aure. Kungiyoyin sun shirya wannan taron ne a […]

COJOYA da Jama’atu sun shirya bita game da gwaji kafin aure
COJOYA da Jama’atu sun shirya bita game da gwaji kafin aure

Kungiyar ci gaban matasa da ake kira COJOYA da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato, tare da hadin gwiwar Kungiyar Jama’atu Nasril Islam, reshen Karamar Hukumar Jos ta Arewa, sun shirya wani taron wayar da kan al’ummar Musulmi kan muhimmancin yin gwaje-gwajen cututtuka kafin a daura aure.

Kungiyoyin sun shirya wannan taron ne a dakin taro na babban masallacin Juma’a da ke garin Jos.

Taron mai taken “Gwaji Kafin Aure A Mahanga ta Kiwon lafiya da mahanga ta addinin Musulunci,”  manyan masana da malaman addinin Musulunci, sun gabatar da jawabai a wajen taron.

Manyan masana kan kiwon lafiya da addinin Musulunci da suka gabatar da jawabi a wajen taron sun hada da Farfesa Ahmad Sabo da Dokta Muhammad Bello da Farfesa  Abdurrahman Lawal  da Dokta Yusuf Abdullahi , dukkansu daga  Jami’ar Jos da Dokta Abdurrahman Zakariyya da Dokta Zuwaira Ahmad  daga  Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Masanan sun yi bayanai kan cututtukan  karya garkuwar jiki  [HIB] da Ciwon Hanta da cutar Sikila da dai sauransu.

Masanan sun cin ma matsaya kan cewa yin gwaji kafin aure, yana da matukar muhimmanci saboda da rashin yin haka yana  kawo wa al’umma damuwa.

Sun yi kira ga  matasa  maza da mata da suke bukatar yin aure, su rika yin  gwaji kafin a daura aure  saboda kare kai daga kamuwa da cututtuka masu barazana ga rayuwarsu da ’ya’yan da  za su haifa.

A nasa jawabin, Shugaban Kungiyar Matasan ta COJOYA, Barista Buhari Ibrahim Shehu ya yi kira ga wadanda suka halacci taron, su kai sakon unguwanninsu don ganin an yi nasara, wajen kare kai daga kamuwa da irin  cututtuka masu barazana ga rayuwar al’umma gaba daya.