Conte ya fara jan ragamar Tottenham da kafar dama

Conte ya samu nasara a wasan farko da ya jagoranci Tottenham a gasar Europa League.

Conte ya fara jan ragamar Tottenham da kafar dama

Antonio Conte

Sabon kocin Tottenham, Antonio Conte ya fara jan ragamar kungiyar da kafar dama, bayan da ya samu nasara a wasan farko da kungiyar ta fafata karkashin jagorancinsa.

Tottenham ta samu nasarar lallasa Vitesse da kwallaye 3-2 a wasan farko da Conte ya jagoranci kungiyar a gasar Europa League a daren ranar Alhamis.

Ana iya tuna cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ce Tottenham ta sanar daukar Antonio Conte a matsayin sabon kocinta da ya maye gurbin wanda ta kora, Nuno Espirito.

Farawa da kafar dama da Conte ya yi na zuwa ne yayin da a mintuna 45 na farkon wasan magoya bayan Tottenham suka yi masa tsayuwar ban girma ganin yadda cikin mintuna 28 kungiyar tasa da ke wasa a gida ta samu nasarar jefa kwallaye 3 rigis a ragar Vitesse.

A shekarar 2016 dai Antonio Conte ya samu nasara a wasan farko da ya jagoranci kungiyar Chelsea, daga bisani kuma ya samu nasara lashe wasanni 13 a jere.

Haka kuma a waccan lokacin kungiyar ta Tottenham da a yanzu yake horaswa ce ta kawo karshen nasarorin da ya jera inda ta doke Chelsea da kwallaye 2-0.