Coronavirus: Karin mutum uku sun mutu a Legas

An samu  karin mutum uku da suka mutu a Legas sakamakon kamuwa da cutar coronavirus, yayin da yawan masu ɗauke da cutar ya kai 235 a jihar. A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a shafinsa na Twitter, kwamishinan lafiya na jihar, Farfesa Akin Abayomi, ya  ce mutum ukun da suka mutu a baya-bayan […]

Coronavirus: Karin mutum uku sun mutu a Legas

‘Yan aikin sa-kai suna feshin maganin kashe kwayoyin cuta a wata makaranta a China (Hoto: STR / AFP)

An samu  karin mutum uku da suka mutu a Legas sakamakon kamuwa da cutar coronavirus, yayin da yawan masu ɗauke da cutar ya kai 235 a jihar.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a shafinsa na Twitter, kwamishinan lafiya na jihar, Farfesa Akin Abayomi, ya  ce mutum ukun da suka mutu a baya-bayan nan babu alamun sun yi tafiya zuwa kasashen ketare.
“Mutune ukun da suka mutu maza ne masu shekaru 51, da 52 da 62, kana daya daga cikin su likita ne da ya dauki cutar a lokacin da yake kula da wasu da suka kamu”.
Farfesa Abayomi ya kara da cewa  labari mai dadin fada shi ne a baya-bayan nan an sallami mutum 16 da suka warke sarai daga cutar, lamarin da ya ba da adadin mutum 85 da suka warke  a jihar ta Legas, yayin da mutum 10  suka mutu a sakamakon annobar.
Zuwa yanzu dai jihar Legas ce kan gaba a Najeriya da yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar – 235 a cikin 407 da suka kamu a Najeriya baki daya.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya