Coronavirus: ‘Abin da ya sa Jigawa ke kula da wadanda suka kamu’
Gwamnatin Jigawa ta ce ta amince ta karbi daya daga cikin mutum biyu da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus daga jihar Kano ne don biyayya ga dokar kasa. Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Gwamnan dai ya ce an gano cewa […]
Gwamnatin Jigawa ta ce ta amince ta karbi daya daga cikin mutum biyu da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus daga jihar Kano ne don biyayya ga dokar kasa.
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.
Gwamnan dai ya ce an gano cewa mutumin ba dan asalin jihar Jigawa ba ne.
“Amma tun da doka ce ta kasa ta ce duk inda aka samu mai cutar a killace shi, jihar jigawa za ta ci gaba da ba shi kulawa har zuwa lokacin da zai warke a sallame shi”, inji Gwamna Badaru.
Ya kuma ce mutum na farko da aka tabbatar ya kamu da cutar wani dan kabilar Ibo ne da ya dawo jihar bayan ya je garinsu ganin gida.
- Coronavirus: An samu karuwar majinyata mafi girma a Najeriya
- ’Yar shekara 15 ta kashe kanta a Jigawa
A cewar gwamnan, an samu mutumin ne a karamar hukumar Kazaure, inda yake sayar da atamfa da leshi da shadda ga masu bukata don yin hidimar sallah.
Gwamna Badaru ya kara da cewa tuni aka killace mutumin don gudun kada ya yada cutar ga sauran jama’ar yankin.
Gwaman ya kuma ce sun zauna da limamai da sarakuna da jami’an tsaro don ganin an toshe duk wata hanya da za a iya bi a shigo jihar.
Sannan ya koka da rashin hadin kan jama’a ta yadda suke amfani da barauniyar hanya idan sun dawo daga ci-rani suna shigewa gidajensu.
Gwamnan ya kuma nuna takaicinsa da yadda bata-gari kan nuna wa baki barauniyar hanya don su kauce wa shingen jami’an tsaro da gwamnati ta kafa don kare lafiyar al’ummar jihar.
Sannan Gwamna Badaru ya ce gwamnati za ta yi iya kokarinta don ganin ta killace duk wanda ya dawo daga tafiya ko yawon ci-rani har tsawon mako biyu.