Coronavirus: Abubuwa sun daidaita a Daura

Harkoki sun koma yadda aka saba a birnin Daura na jihar Katsina bayan fargabar da jama’a da dama suka shiga, jin labarin rasuwar wani likita da aka ce ya kamu da cutar coronavirus. Tun da farko dai hukumomi sun yi kira ga mutane duk wanda ya san ya yi mu’amala da likitan, Dokta Aliyu Yakubu, […]

Coronavirus: Abubuwa sun daidaita a Daura

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari

Harkoki sun koma yadda aka saba a birnin Daura na jihar Katsina bayan fargabar da jama’a da dama suka shiga, jin labarin rasuwar wani likita da aka ce ya kamu da cutar coronavirus.

Tun da farko dai hukumomi sun yi kira ga mutane duk wanda ya san ya yi mu’amala da likitan, Dokta Aliyu Yakubu, ya kai kan shi.

Sai dai har zuwa yanzu ba a bayyana inda mutanen suke ba ko kuma yadda aka yi da su.

Har zuwa lokacin rubuta wannan labari dai babu wani wuri na musamman da aka ware a garin na Daura don killace wadanda ake tunanin yiwa gwaji saboda sun yi hulda da likitan.

Abin da kawai yake tabbatacce shi ne zuwan likitocin da gwamnatin jiha ta tura don zakulo mutanen da ake hasashen sun yi mu’amala da shi.

Sai dai kuma Aminiya ta ga yadda aka dauki matakan tsaro a gidan marigayin ta hanyar killace wajen, domin da gidan da asibitin duk a wuri daya suke—saman bene na iyalin shi, kasa kuma asibiti.

Da maraicen Talata ne dai Gwamna Aminu Bello Masari na jihar ta Katsina ya bayyana rasuwar likitan, wanda ya riga mu gidan gaskiya tun ranar Asabar.

Sai dai ba a tabbatar yana dauke da cutar coronavirus ba sai da sakamakon gwajin da aka yi masa ya fito bayan kwana uku, kasancewar babu cibiyar gwaji a fadin jihar.

Da ma dai mutane da dama sun yi ta kira a kafa cibiyar gwajin a jihar Katsina.

Shugaban reshen Katsina na kungiyar wakilan kafafen yada labarai na Najeriya Kwamared Abdulhamid Sabo, na cikin mutanen da suka yi kira ga gwamnatin tarayya da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) da su samar da cibiyar binciken cutar a jihar domin samun sauki tare da daukar matakin gaugawa a cikin lokaci ba sai abin ya yi nisa ba.

“Yanzu da a ce akwai wurin binciken wannan cuta a jihar da tuni an gano matsalar wancan likitan an kuma san matakin da ya kamata a dauka tun kafin ya mutu.

“Saboda haka, muke neman hukumar ta NCDC da ta yi gaugawar samar da wajen wannan bincike domin samun saukin zuwa inda za a yo binciken da ba za a iya samun sakamakonsa a cikin lokaci ba saboda nisan inda za a kai,” in ji Kwamared Sabo.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno