Coronavirus: Adadin wadanda suka kamu ya karu da 17
Mutum 17 ne aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya a baya-bayan nan. Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ce ta fadi haka a wata sanrwa da ta wallafa a shafinta na Twitter. “An ba da rahoton sabbin kamuwa da coronavirus kamar haka: takwas a Legas, uku a Katsina, biyu […]
Mutum 17 ne aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya a baya-bayan nan.
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ce ta fadi haka a wata sanrwa da ta wallafa a shafinta na Twitter.
“An ba da rahoton sabbin kamuwa da coronavirus kamar haka: takwas a Legas, uku a Katsina, biyu a Yankin Babban Birnin Tarayya, daya a Neja, daya a Kaduna, daya a Anambra, daya kuma a Ondo”, inji NCDC.
Wannan ne ya kai jimillar wadanda aka tabbatar sun kamu a Najeriya 305 zuwa karfe 9.30 na daren 10 ga watan Afrilu.
“Daga cikinsu an sallami mutum 58, yayin da wasu bakwai kuma suka riga mu gidan gaskiya”, inji NCDC.
Jihar Legas ce dai ke kan gaba da yawan wadanda suka kamu yayin da Yankin Babban Birnin Tarayya ke rufa mata baya,