Coronavirus: An haramta taron ibada a masallatai da coci a Legas
Gwamnatin jihar Legas ta haramta taron ibada a daukacin fadin jihar a wani mataki na kare yaduwar cutar murar mashako ta Coronavirus. Kwamishinan al’amuran cikin gida na jihar Anofiu Elegushi, ne ya bayyana hakan a yau Laraba bayan wani taron da ya yi da masu ruwa da tsaki a al’amuran addinai a jihar taron da […]
Gwamnan Legas Sanwo-Olu lokacin da yake bayani
Gwamnatin jihar Legas ta haramta taron ibada a daukacin fadin jihar a wani mataki na kare yaduwar cutar murar mashako ta Coronavirus.
Kwamishinan al’amuran cikin gida na jihar Anofiu Elegushi, ne ya bayyana hakan a yau Laraba bayan wani taron da ya yi da masu ruwa da tsaki a al’amuran addinai a jihar taron da ya sami halarcin babban limamin jihar Sheikh Suleiman Abou Nolla da shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN reshen jihar AlexanderBamgbola.
Kwamishinan ya shaida cewa gwamnatin ta dauki matakin ne domin dakile yaduwar cutar coronavirus.