Coronavirus: An kaddamar da sabon tsarin kiwon lafiya a Legas

Gwamnatin jihar Legas ta kaddamar da manhajar kiwon lafiya ta tafi-da-gadanka wacce aka yiwa lakabi da ‘EKO TELEMED’ a wani yunkuri na gwamnatin domin kiyaye yaduwar annobar a jihar. Tsarin kiwon lafiyar wanda ya fara aiki ranar 22 ga watan Afrilu zai yi mako takwas ana gudanarwa inda za a kammala shirin a ranar 17 […]

Coronavirus: An kaddamar da sabon tsarin kiwon lafiya a Legas

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu

Gwamnatin jihar Legas ta kaddamar da manhajar kiwon lafiya ta tafi-da-gadanka wacce aka yiwa lakabi da ‘EKO TELEMED’ a wani yunkuri na gwamnatin domin kiyaye yaduwar annobar a jihar.
Tsarin kiwon lafiyar wanda ya fara aiki ranar 22 ga watan Afrilu zai yi mako takwas ana gudanarwa inda za a kammala shirin a ranar 17 ga watan Yuli na wannan shekara.
Ma’aikatar lafiya ta jihar Legas ce ta sanar da haka a shafinta na Twitter  da safiyar Laraba.
Sanarwar. wada babbar sakatariyar ma’aikatar Dakta Emmanuella Zamba ta sanyawa hannu ta ce mazauna jihar ta Legas za su amfana da tsarin kiwon lafiyar wanda ba ya bukatar kulawar gaggawa ta hanyar  kiran wayar salula ko kuma ta yin kiran bidiyo.
Ta kara da cewa manhajar za ta bai wa mazauna Legas damar zantawa da likitoci a manyan harsunan kasar nan guda uku da kuma Ingilishi wato harsunan Ingilishi da Hausa da Yarbanci da kuma harshen Ibo, kana likitocin da jami’an kiwon lafiyar  za su kasance cikin aikin agaza wa jama’a  a ko wane lokaci a tsawon makawanni takwas na shirin yayin da mahukuntan jihar ke ci gaba da kokarin kawar da annobar Covid-19.
Dakta Zamba ta kara da cewa duk mutumin da ke fama da wani ciwo da ba shi da alaka da coronavirus zai iya kiran lambar wayar salula ta 08000EKOMED ko 08000356633 wace ake kira a kyauta domin samun shawarwari daga kwararrun likitoci, kana ga mutanen da ke da cututtuka masu alamar Coronavirus za a mika su ne ga cibiyoyin da aka tanadar a jihar domin yin gwajin cutar tare da killace su.
“Idan akwai bukatar duba lafiyar su bayan likitocin sun ba su shawara, wadanda ciwonsu ba shi da alaka da coronavirus za a tura su cibiyar kula da lafiya da ma’aikatar kiwon lafiya ta Legas wato (LSHS) ta tanadar.
“Wannan shiri ne da  zai bai wa al’umma damar samun kulawa ta fannin kiwon lafiyarsu duba da kalubalen da ake fuskanta a sakamakon hana zirga-zirga in ba da kwakkwaran dalili ba.
“Kana wannan shiri zai taimaka wajen  saukaka gano masu coronavirus tare da yi masu gwaji da killace su a wuraren da aka tanada domin hakan, wannan shiri ne da zai rage zirga-zirga  ko kuma cunkoson jama’a da yawan mace-mace da kuma hadarin yaduwa ko kamuwa da cutar”, inji Dakta Zamba.
A karshe ta ta yi kira ga mazauna Legas da su tabbatar sun ci gajiyar shirin da aka samar domin su domin yin haka ne zai bai wa gwamnatin jihar damar kare rayukan al’ummar jihar.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya