Coronavirus: An sallami ragowar masu cutar a Kebbi

An sallami mutum biyu da suka rage masu dauke da cutar coronavirus a jihar Kebbi bayan sun warke daga annobar. Ragowar mutum biyun an sallame su ne a yau Alhamis bayan sakamakon gwajin da aka yi musu ya nuna sun warke. Kwamishinan Lafiyan jihar Kebbi, Jafar Muhammad ya sanar da haka a sashen killace masu […]

Coronavirus: An sallami ragowar masu cutar a Kebbi

Kwamishinan Lafiya na jihar Kebbi Alhaji Jaafar Mohammed (Hoto: NAN)

An sallami mutum biyu da suka rage masu dauke da cutar coronavirus a jihar Kebbi bayan sun warke daga annobar.

Ragowar mutum biyun an sallame su ne a yau Alhamis bayan sakamakon gwajin da aka yi musu ya nuna sun warke.

Kwamishinan Lafiyan jihar Kebbi, Jafar Muhammad ya sanar da haka a sashen killace masu coronavirus a Cibiyar Lafiya ta Jihar da ke Kalgo.

“Za su koma su ci gaba da mu’amala a cikin al’umma domin gwaje-gwajen da aka kara yi sun tabbatar da warkewarsu,” inji shi.

Kwamishinan ya kara da cewa yanzu ke nan babu sauran mai dauke da cutar ta COVID-19 a fadin jihar.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar Taraba ta sallami mutun na karshe mai cutar bayan ya warke.

An sanya dokar hana fita a wasu yankunan Taraba

Jami’an NSCDC sun daƙile harin ’yan bindiga a Kano

Matsalar Tsaro: Ku sayi makamai don kare kanku — Sarkin Argungun

Mai juna biyu na wata 8 ta shigar da ƙarar neman saki