Coronavirus: Karin mutum 155 sun kamu, 4 sun mutu
An samu karin mutum 155 da suka kamu da cutar coronavirus, mutum 4 kuma sun mutu.
A ranar Laraba an samu karin mutum hudu da suka mutu sakamakon cutar coronavirus yayin karin mutum 155 suka kamu da cutar a Najeriya.
Alkaluman da hukumar NCDC mai yaki da cututtuka masu yaduwa na ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba sun nuna jimillar wadanda cutar ta kashe a fadin kasar sun kai 1,155 tun daga watan Fabrairun 2020 da ta bulla.
- KAROTA za ta dauki karin ma’aikata
- ASUU ta gindaya wa Gwamnati sharadin janye yajin aiki
- Gwamnan Jigawa ya gabatar da kasafin kudi na 2021
Haka kuma karin mutum 155 sun harbu da cutar a jihohi 10 da suka hada da mutum 85 a Legas, 23 a Abuja, 18 a Ondo, mutum 8 a Ogun, 5 a Kaduna, Oyo da Taraba mutum biyar-biyar, Kano mutum 3, Ribas mutum 2, da kuma Bauchi, mutum 1.
Ya zuwa yanzu dai cutar ta harbi mutum 63,328 a Najeriya yayin da aka sallami mutum 59,675 da suka warke daga cibiyoyin killace masu cutar.
Da wannan sabbin alkaluma da aka fitar, jihar Legas ce a kan gaba ta fuskar yawan masu cutar da suk kai 21,483 sai kuma Abuja a mataki na biyu da mutum 6,165.