Coronavirus: An samu karin mutum shida

An samu karin mutum shida da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus, lamarin da ya sai adadin wadanda suka kamu a Najeriya ya kai 190. Gaba daya mutum shidan dai a jihar Osun suke, kamar yadda Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar a shafinta na Twitter. “Zuwa karfe 11.00 […]

Coronavirus: An samu karin mutum shida

Wani jami’in Ma’aikatar Kula da muhalli ta Jihar Borno yana yin feshin maganin kashe kwayoyin cuta a wani masallaci a Maiduguri da nufin hana COVID-19 yaduwa (Hoto: AUDU MARTE / AFP)

An samu karin mutum shida da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus, lamarin da ya sai adadin wadanda suka kamu a Najeriya ya kai 190.

Gaba daya mutum shidan dai a jihar Osun suke, kamar yadda Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar a shafinta na Twitter.

“Zuwa karfe 11.00 na ranar 3 ga watan Afrilu an tabbatar da mutum 190 sun kamu da COVID-19 a Najeriya. An sallami 20 daga cikinsu yayin da biyu suka riga mu gidan gaskiya”, inji sanarwar.

Har yanzu dai jihar Legas ce ke kan gaba wajen yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da kashi 54 cikin 100, yayin da Yankin Babban Birnin Tarayya ke biye mata da kashi 21 cikin 100.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50