Coronavirus: An samu karin wadanda suka kamu 91
Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya karu da mutum 91. Wata sanarwa da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta wallafa a shafinta na Twitter ya nuna cewa hakan ya kai adadin wadanda aka tabbatar sun kamu din zuwa 1,273. “Zuwa karfe 11.50 na daren 26 […]
Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya karu da mutum 91.
Wata sanarwa da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta wallafa a shafinta na Twitter ya nuna cewa hakan ya kai adadin wadanda aka tabbatar sun kamu din zuwa 1,273.
“Zuwa karfe 11.50 na daren 26 ga watan Afrilu, an samu mutum 1,273 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya”, inji sanarwar.
- COVID-19: El-Rufai ya tsawaita dokar zaman gida da kwana 30
- Coronavirus: Majinyata biyu sun shiga buya a Borno
Arba’in da uku daga cikin mutanen 91 a jihar Legas suke, takwas a Sakkwato, shida a Taraba, biyar a Kaduna, biyar a Gombe, uku a Ondo, uku a Yankin Babban Birnin Tarayya.
Jihohin Oyo da Edo da Ribas da Bauci ma na da mutum uku-uku, Osun na da biyu, sannan Akwa Ibom, da Bayelsa da Ebonyi da Kebbi na da guda ko wacce.
Jihohin da suka shiga lissafi a baya-bayan nan su ne Taraba, da Bayelsa, da Ebonyi, da kuma Kebbi.
Mutum tara jihohin suka raba a tsakaninsu, yayin da Taraba ke da kaso mafi tsoka na mutum shida a tashin farko.
Galibin jihohi dai sun ayyana dokar hana fita a yankunan su da nufin hana cutar yaduwa.