Coronavirus: An samu karuwar majinyata mafi girma a Najeriya

An samu karuwa mafi girma a cikin sa’o’i 24 ta mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya. A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter da tsakar daren Lahadi, Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an samu rahoton sabbabin kamu har mutum 86. Saba’in […]

Coronavirus: An samu karuwar majinyata mafi girma a Najeriya

Wani dakin killace masu Coronavirus

An samu karuwa mafi girma a cikin sa’o’i 24 ta mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter da tsakar daren Lahadi, Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an samu rahoton sabbabin kamu har mutum 86.

Saba’in daga cikin mutanen dai an same su ne a jihar Legas, bakwai a Yankin Babban Birnin Tarayya, uku a Katsina, uku a Akwa Ibom, daya a Jigawa, daya a Bauchi, daya a Borno.

A cewar hukumar, “Zuwa karfe 11.50 na daren 19 ga watan Afrilu, mutanen da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya sun kai 627.

“Daga cikinsu an sallami 170 bayan sun warke, yayin da mutum 21 suka riga mu gidan gakiya”.

Hakan na nufin a yanzu haka akwai mutane 436 da ke jinya bayan an tabbatar sun kamu.

Har yanzu dai jihar Legas ce ke kan gaba a yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da mutum 376, Abuja na biye da ita da mutum 88, yayin da Kano ke rufa musu baya da mutum 36.

Jihohin da suka shiga lissafi a baya-bayan nan su ne Jigawa da Borno—yayin da Jigawa ke da mutum biyu, Borno na da mutum daya.

A halin da ake ciki dai jihohin Legas da Ogun da ma Yankin Babban Birnin Tarayya na karkashin dokar hana fita kwatakwata a yunkurin gwamntai na hana yaduwar cutar.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya