Coronavirus: An samu mutuwa ta farko a Kano
A karo na farko an samu rahoton mutuwar mutum guda sakamakon kamuwa da cutar coronavirus a jihar Kano. Ma’aikatar lafiya ta jihar ce dai ta sanar da hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter. “Zuwa karfe 11.55 na daren Laraba 15 ga watan Afrilu an samu mutuwar mutum guda sakamakon kamuwa […]
A karo na farko an samu rahoton mutuwar mutum guda sakamakon kamuwa da cutar coronavirus a jihar Kano.
Ma’aikatar lafiya ta jihar ce dai ta sanar da hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.
“Zuwa karfe 11.55 na daren Laraba 15 ga watan Afrilu an samu mutuwar mutum guda sakamakon kamuwa da #COVID-19 a jihar Kano”, inji sanarwar.
Ma’aikatar ta kuma ce zuwa wannan lokacin dai mutum 21 ne jimilla aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar.
- COVID-19: Farashin kaya ya tashi a Kano
- Darussa uku da Najeriya ka iya koya daga annobar coronavirus
Sai dai kuma zuwa yanzu Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ba ta tabbatar da wadannan alkaluma ba.
A lissafin NCDC, zuwa karfe 11.20 na daren Larabar mutum 16 aka tabbatar sun kamu a jihar ta Kano.
Ranar Asabar din ta gabata ne dai aka sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar, wani tsohon jami’in diflomasiyya da aka ce ya yi tafiye-tafiye zuwa Legas da Abuja da Kaduna.
Zuwa yanzu babu cikakken bayani a kan wanda cutar ta coronavirus ta yi ajalinsa.