Coronavirus: An samu sabbin kamuwa 108 a Najeriya

Mutane 108 ne aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a baya-bayan nan a Najeriya, inji Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC. Hukumar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter. Saba’in da takwas daga cikin mutanen a jihar Legas suke, 14 a Yankin Babban Birnin Tarayya, […]

Coronavirus: An samu sabbin kamuwa 108 a Najeriya

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu lokacin da ya ziyarci wani wajen killace masu coronavirus

Mutane 108 ne aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a baya-bayan nan a Najeriya, inji Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.

Saba’in da takwas daga cikin mutanen a jihar Legas suke, 14 a Yankin Babban Birnin Tarayya, hudu a Gombe, uku a Borno, biyu a Akwa Ibom, daya a Kwara.

Sai kuma jihar Filato, inda aka tabbatar da samun wanda ya kamu a karo na farko, mai mutum daya.

“Zuwa karfe 11.30 na daren 23 ga watan Afrilu, an tabbatar da mutane 981 sun kamu da cutar COVID-19 a Najeriya”, inji hukumar.

Hukumar ta kuma ce an sallami mutum 197 daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu, yayin da 31 suka riga mu gidan gaskiya.

 

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya