Coronavirus: Ana bibiyar mutum 692 a Kano
Kwamitin kar-ta-kwana a kan yaki da annobar coronavirus na Kano ya ce yana bibiyar mutane 692 wadanda ake zargin sun kamu da cutar coronavirus ko sun yi mu’amala da wadanda suka a fadin jihar. Daya daga cikin mambobin kwamitin, Dokta Tijjani Usaini, ya shaida wa manema labarai cewa sama da 400 daga cikin mutanen ne […]
Kwamitin kar-ta-kwana a kan yaki da annobar coronavirus na Kano ya ce yana bibiyar mutane 692 wadanda ake zargin sun kamu da cutar coronavirus ko sun yi mu’amala da wadanda suka a fadin jihar.
Daya daga cikin mambobin kwamitin, Dokta Tijjani Usaini, ya shaida wa manema labarai cewa sama da 400 daga cikin mutanen ne ake zargin sun kamu da cutar.
“A yanzu haka akwai mutane 426 wadanda ake zargin suna dauke da cutar a jihar; haka kuma akwai mutane 266 wadnda ake zargin sun yi mu’amala da su, don haka kwamitin ke bibiyarsu don ganin an tantance su”, inji shi.
A cewar shi, bibiyar mutanen da suka yi mu’amala da masu dauke da cutar yana daga cikin aikin da kwamitin ya fi ba muhimmanci don murkushe cutar ba tare da samun burbushinta a tsakanin alumar jihar ba.
A yanzu haka dai kididdigar Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta nuna cewa mutum 73 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar Kano.