Coronavirus: Atiku ya bukaci a maida hankali a Kano

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin tarayya da sauran hukumomin da suke taka rawa a yaki da cutar coronavirus a Najeriya da su hada hannu da gwamnatin jihar Kano wajen dakile yaduwar cutar a jihar. Atiku Abubakar, ya ce akwai bukatan hukumomi su maida hankali akan annobar a Kano saboda kiyaye yaduwar […]

Coronavirus: Atiku ya bukaci a maida hankali a Kano

Atiku Abubakar, dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin tarayya da sauran hukumomin da suke taka rawa a yaki da cutar coronavirus a Najeriya da su hada hannu da gwamnatin jihar Kano wajen dakile yaduwar cutar a jihar.

Atiku Abubakar, ya ce akwai bukatan hukumomi su maida hankali akan annobar a Kano saboda kiyaye yaduwar ta zuwa jihohi masu makwabtaka da ita da kuma sauran jihohin Arewacin kasar.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya  bayyana hakan ne a wani sako da ya fitar a ranar Juma’a ta hannun mai ba shi shawara kan yada labarai, Paul Ibe inda ya ce lamarin a Kano zai kasance zakaran gwajin dafi akan nasarar da ake samu a yaki da cutar a Najeriya.

Ya kara da cewa, ya kamata a yi kokarin bayar da cikakken bayani akan halin da ake ciki saboda kwanciyar hankalin jama’ar Kano.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su dauki matakan kariya kamar yadda hukumomin yaki da cutar suka zayyana a daidai lokacin da ake shirin sassauta dokar zaman gida.

Atiku Abubakar, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a zaben shekarar 2019, ya kuma jajantawa iyalan Chief Raymond Dokpesi wadanda suka harbu da cutar Coronavirus.