Coronavirus ba ta kama ni ba —Ahmed Musa

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya, Ahmed Musa, ya musanta labarin da ke wadari a kafafen sadarwa na zamani cewa ya kamu da cutar coronavirus. Ahmed Musa ya karyata labarin ne, wanda ya kira labaran bogi, a shafinsa na Twitter. “Ku yi watsi da duk wani labarin karya da cewa ni […]

Coronavirus ba ta kama ni ba —Ahmed Musa

Ahmed Musa tare da iyalansa (Hoto: Ahmed Musa/Twitter)

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya, Ahmed Musa, ya musanta labarin da ke wadari a kafafen sadarwa na zamani cewa ya kamu da cutar coronavirus.

Ahmed Musa ya karyata labarin ne, wanda ya kira labaran bogi, a shafinsa na Twitter.

“Ku yi watsi da duk wani labarin karya da cewa ni ko iyalina mun kamu da cutar COVID-19.

“Mun dai killace kanmu na tsawon mako biyu kasancewar ba mu jima da shigowa ba daga Saudi Arebiya”, inji Ahmed Musa, wanda ke wasa a kungiyar kwallon kafa ta Al-Nasr da ke Saudi Arebiya.

Ya kuma mayar da martini ga wani sakon Twitter (wanda aka cire daga bisani) da ke ambato shi yana cewa ya kamu: “Cire wannan labarin bogin don Allah”.

Dan wasan ya kuma yi kira ga masu bibiyar sa a shafin na Twitter da su bi tsarin nisa da juna su kuma kaurace wa labarin bogi.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya