Coronavirus: Bankin UBA zai ba da gudummawa mai tsoka
Bankin UBA ya ce zai samar da agajin Naira biliyan biyar don taimaka wa kasashen Afirka su yaki cutar Coronavirus. Bankin ya sanar da haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter. “Don zaburar da yunkuri na bai-daya da ake yi a fadin Afirka don yakar cutar Coronavirus, za mu samar […]
Bankin UBA ya ce zai samar da agajin Naira biliyan biyar don taimaka wa kasashen Afirka su yaki cutar Coronavirus.
Bankin ya sanar da haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
“Don zaburar da yunkuri na bai-daya da ake yi a fadin Afirka don yakar cutar Coronavirus, za mu samar da Naira biliyan biyar ga asusun tallafin yaki da COVID-19 na Afirka”.
A cewar bankin, wannan tallafi zai samar da taimakon da ake matukar bukata a Najeriya da wasu kasashen Afirka 19 ta hanyar samar da kayan agaji, da na aikin jinya, da tallafin kudi ga gwamnatoci.
UBA ya kara da cewa za a bai wa Jihar Legas Naira biliyan daya daga cikin kudin, za a ba Abuja miliyan 500, sauran jihohin Najeriya kuma za a raba masu biliyan daya.
- Mutum shida sun warke daga cutar Coronavirus a Legas
- Coronavirus: Gwamnatin Neja ta dakatar da sallar Juma’a
Su kuma sauran kasashen Afirka dake da rassan bankin za su samu Naira biliyan daya da rabi, za kuma a kashe biliyan daya wajen samar da kayan aiki ga cibiyoyin kiwon lafiya.
A ranar Laraba tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya yi alkawarin bayar da gudummawar Naira miliyan 50 don tallafa wa gwamnatin Najeriya a yakin da take yi da cutar.
A wata sanarwa da ya fitar, Atiku ya yaba da matakan da aka dauka ciki har da takaita fita, amma ya yi kira da a samar wa talakawa wani tallafi saboda galibi sai sun fita suke samun na abinci.
A watan jiya ne dai gwamnatin Najeriya, ta bakin Babban Sakatare a Ma’aikatar Lafiya Abdullahi Abdullaziz Mashi, ta ba da sanarwar fitar da Naira miliyan 386 domin hana yaduwar cutar.
Tun da farko dai yayin da yake wani jawabi a zauren Majalisar Dattawa, Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya ce gwamnatin ta kasafta Naira miliyan 620 ga wani asusu na musamman don daukar matakan hana cutar yaduwa.
Zuwa karfe 11.25 na daren Laraba dai alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa sun cewa mutm 51 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya.