Coronavirus: Buhari zai yi jawabi ga ‘yan Najeriya yau

Fadar shugaban Najeriya ta ce, shugaba Buhari zai gabatar da jawabi ga ‘yan kasar da yammacin yau  Litinin da misalin karfe 7 na yamma. Mai ba shugaba Buhari shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ne ya fitar da sanarwar cewa shugaban zai gabatar da jawabin ne da misalin karfe 7:00 na yamma wanda za […]

Coronavirus: Buhari zai yi jawabi ga ‘yan Najeriya yau

Shugaba muhammadu Buhari na Najeriya

Fadar shugaban Najeriya ta ce, shugaba Buhari zai gabatar da jawabi ga ‘yan kasar da yammacin yau  Litinin da misalin karfe 7 na yamma.

Mai ba shugaba Buhari shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ne ya fitar da sanarwar cewa shugaban zai gabatar da jawabin ne da misalin karfe 7:00 na yamma wanda za a watsa kai tsaye a kafofin watsa labarai na kasar.

Ana kyautata zaton shugaba Buhari zai yi jawabi ne akan annobar coronavirus  da kuma matakan da gwamnati ke dauka, inda ake sa ran watakila ya tsawaita dokar hana fita da shugaban ya kafa a jihohin Lagos da Ogun da kuma birnin tarayya Abuja.

Ma’aikatan Abuja ba sa sona — Wike

Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da ofishin ’yan sanda

Gwamnati ta ƙara albashin sojoji — Ministan Tsaro

’Yan bindiga sun kashe mutum 3 a wani sabon hari a Filato