Coronavirus: Bukatar gwamnati ta tallafa wa manoman Jigawa
Gwamnatin Jihar Jigawa na bukatar ta sama wa manoma kayan noma da irin shukawa don rage tasirin da cutar coronavirus da suka fuskanta sakamakon dokar kulle. Malami a Jami ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse (FUD) ya jaddada bukatar gwamnatin jihar ta tallafa wa manoma da irin shuka mai yi da wuri kasancewar sun samu […]
Gwamnatin Jihar Jigawa na bukatar ta sama wa manoma kayan noma da irin shukawa don rage tasirin da cutar coronavirus da suka fuskanta sakamakon dokar kulle.
Malami a Jami ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse (FUD) ya jaddada bukatar gwamnatin jihar ta tallafa wa manoma da irin shuka mai yi da wuri kasancewar sun samu nakasun tattalin arziki sakamakon dokar da ta dakatar da harkoki.
Ado Garba Jangargari wanda masani ne a fannin noma ya ce a matsayin gwamnatin Jigawa ta manoma, akwai bukatar gwamnatin ta agaza wa masu sana’ar.
Ya kuma bayyana damuwa game da matsalolin da cutar coronavirus ta haifar wa manoma a Najeriya, wadda ya ce tayi sanadiyyar rashin yin shuka a kan lokaci.
- Coronavirus: ‘Mutum 800 ne za su iya kamuwa a Jigawa’
- An dage dokar kulle saboda sallar Idi a Jigawa
- Motocin kwashe shara uku ne kacal a Jigawa
Rashin yin shuka a kan lokaci babbar matsala ga manoma inji shi, don haka akwai bukatar gwamnati ta tallafa da kayan da manoma ke bukata a matsayin tallafin coronavirus.
Yin hakan, yana ganin zai taimaka wajen rage wa al’umma halin matsin rayuwa da ake ciki sakamakon bullar cutar.