Coronavirus: ‘Dalilin dakatar da komai a Filato’

Daya daga cikin manyan dalilan da suka sa aka hana fita kwatakwata har tsawon mako guda a jihar Filato shi ne samun damar yin feshi a kasuwanni da wuraren taruwar al’umma. Gwamnan jihar Simon Lalong ne ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da aikin  feshin na maganin kashe kwayoyin cuta a Jos da […]

Coronavirus: ‘Dalilin dakatar da komai a Filato’

Ma;aikata na shirin fara feshin maganin kashe kwayoyin cuta a Jos, babban birnin jihar Filato

Daya daga cikin manyan dalilan da suka sa aka hana fita kwatakwata har tsawon mako guda a jihar Filato shi ne samun damar yin feshi a kasuwanni da wuraren taruwar al’umma.

Gwamnan jihar Simon Lalong ne ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da aikin  feshin na maganin kashe kwayoyin cuta a Jos da kewaye.

Gwamnan ya kaddamar da aikin ne a babbar kasuwar Taminus da ke tsakiyar birnin na Jos, inda ya ce duk da ba a samu wanda ya kamu da cutar a jihar ba, gwamnati ba za ta nade hannu ba tare ta tashi ta dauki matakan kariya ba.

“Don haka muka kafa dokar hana fita muka kuma rufe jihar nan gaba daya, domin a yi feshin kashe cututtuka a dukkan kasuwanni da hanyoyi da wuraren taruwar jama’a da ke jihar nan.

“Don haka muna kira ga al’ummar jihar nan su zauna a gidajensu, domin ganin an sami nasarar wannan aiki’’, inji Mista Lalong.

Hotuna: Yadda dokar hana fita ta kasance a Plateau

COVID-19: ‘Najeriya za ta shiga makwanni 2 mafiya hadari.’

Ya kuma ce gwamnati ta shirya tunkarar dukkan wani rahoton bullar wannan cuta a jihar,  don ganin an dauki matakin magance ta nan take.

Gwamnan ya kara da cewa nan da ‘’yan kwanaki za a bude cibiyar gwajin cutar a jihar Filato.

Da tsakar daren Alhamis ne dai dokar hana fitar ta fara aiki.

 

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno