Ganduje zai sassauta dokar kulle idan ana bin matakan kariya

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce muddin al’ummar jihar za su kiyaye matakan kariya daga cutar coronavrus, zai sassauta dokar kulle a jihar. Ganduje ya ce dokar kullen ba ta dindindin ba ce, matukar za a kiyaye da ka’idojin kariya daga cutar. “Idan mutane sun kiyaye matakan kariya za mu sassauta dokar […]

Ganduje zai sassauta dokar kulle idan ana bin matakan kariya

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce muddin al’ummar jihar za su kiyaye matakan kariya daga cutar coronavrus, zai sassauta dokar kulle a jihar.

Ganduje ya ce dokar kullen ba ta dindindin ba ce, matukar za a kiyaye da ka’idojin kariya daga cutar.

“Idan mutane sun kiyaye matakan kariya za mu sassauta dokar kullen, abin da ake bukata shi ne a kiyaye matakan kariya domin gujewa yaduwar cutar”, inji Gwamna Ganduje a wata sanarwar gwamnati.

A sanarwar, mai magana da yawun gwamnan, Abba Anwar, ya ce akwai wasu ‘yan kasuwa a jihar Kano da suka koma cikin unguwani suna ci gaba da gudanar da kasuwancinsu tun bayan   da aka rufe kasuwannin jihar domin hana yaduwar cutar, ba tare da bin matakan kariyar ba.

Ya ce duk da cewa al’umma na da ‘yancin walwala da gudanar da harkokinsu na yau da gobe, hakan ba zai zamo dalilin da zai sanya su cutar da kan su, su kuma cutar da jama’a ta hanyar yada cutar ba.

“Don haka kamata ya yi mutum ya san mahimmancin  rayuwarsa da ta iyalansa da al’ummar gari baki daya, ya kame kansa a gida, ya kuma bi ka’idojin kare yaduwar cutar domin ya zauna lafiya”.

Abba Anwar ya kara da cewa gwamnan jihar Kano ya yi wata ganawa ta kafar bidiyo da wasu dattawan jihar a karkashin jagorancin A.B. Mahmud, wadanda suka nuna goyon bayan su ga gwamnan a yakin da yake yi na dakile yaduwar annobar, sun kuma yi na’am da matakan kare al’umar jihar da gwamnatin Ganduje ke dauka.

Ya kara da cewa gwamnatin Kano na aiki tukuru domin samar da cibiyoyin gwajin cutar a kananan hukumomin 36 na jihar, domin gano yadda cutar ke yaduwa a cikin al’uma tare da daukar matakan dakile ta.