Coronavirus: Gwamnatin Najeriya ta bada umarnin rufe jami’o’i da sauran makarantu

A ci gaba da matakan da Gwamnatin Tarayya ke dauka domin dakile yaduwar annobar coronavirus, gwamnatin Najeriya ta bada umarnin rufe daukacin makarantu a fadin kasar wadanda suka hadar da jami’o’i da manyan makarantu na gaba da sakandare da makarantun sakandare da na firamare. Sakataren ma’aikatar ilimi ta kasa Sonny Echono, ne ya bada tabbacin […]

Coronavirus: Gwamnatin Najeriya ta bada umarnin rufe jami’o’i da sauran makarantu

A ci gaba da matakan da Gwamnatin Tarayya ke dauka domin dakile yaduwar annobar coronavirus, gwamnatin Najeriya ta bada umarnin rufe daukacin makarantu a fadin kasar wadanda suka hadar da jami’o’i da manyan makarantu na gaba da sakandare da makarantun sakandare da na firamare.

Sakataren ma’aikatar ilimi ta kasa Sonny Echono, ne ya bada tabbacin hakan a yau Alhamis.

A cikin kwanaki ukun da suka shude mahukunta a matakin jihohi da tarayyar Najeriya na ci gaba da daukar matakan kariya don dakile cutar coronavirus.