Coronavirus: Gwamnatin Neja ta dakatar da sallar Juma’a

Gwamnatin Neja ta bayar da umarnin dakatar da tarukan ibada a dukkan masallatan Juma’ar jihar da nufin hana cutar Coronavirus yaduwa. Hakan dai na nufin da wannan umarni na gwamnati ba za a gudanar da sallar Juma’a ba a fadin jihar. Sanarwar dakatarwar ta fito ne daga Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane. A cewarsa, […]

Coronavirus: Gwamnatin Neja ta dakatar da sallar Juma’a

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello

Gwamnatin Neja ta bayar da umarnin dakatar da tarukan ibada a dukkan masallatan Juma’ar jihar da nufin hana cutar Coronavirus yaduwa.

Hakan dai na nufin da wannan umarni na gwamnati ba za a gudanar da sallar Juma’a ba a fadin jihar.

Sanarwar dakatarwar ta fito ne daga Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane.

A cewarsa, wajibi ne gwamnati ta yi aiki kafada da kafada da shugabannin addini da sauran masu ruwa da tsaki don ganin an yi dukkan mai yiwuwa an hana cutar ta COVID-19 shiga jihar balle ta samu wurin zama.

Tun a makon jiya ne dai hukumomi a Najeriyar suka fara kira ko bayar da umarni ga al’ummominsu da su hakura da tarukan addini a masallatan Juma’a da majami’u don hana cutar yaduwa.

Ma’aikatan Abuja ba sa sona — Wike

Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da ofishin ’yan sanda

Gwamnati ta ƙara albashin sojoji — Ministan Tsaro

’Yan bindiga sun kashe mutum 3 a wani sabon hari a Filato