Coronavirus: Karin mutum 196 sun kamu a Najeriya
A kwana na biyu a jere an samu karuwar mutum sama da 150 da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya. Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) sun nuna cewa a ranar Laraba an samu mutum 196 da aka tabbatar sun kamu, karin mutum guda a kan adadin da […]
A kwana na biyu a jere an samu karuwar mutum sama da 150 da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya.
Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) sun nuna cewa a ranar Laraba an samu mutum 196 da aka tabbatar sun kamu, karin mutum guda a kan adadin da aka samu kwana guda kafin nan.
Da wannan sabon lissafin ne hukumar ta nuna cewa, “Zuwa karfe 11.55 na daren 29 ga watan Afrilu, mutum 1,728 ne aka tabbatar da sun kamu da COVID-19 a Najeriya”.
Daga cikin wadannan mutum 196 da aka tabbatar sun kamu a baya-bayan nan dai, 87 a jihar Legas suke, 24 a Kano, 18 a Gombe, 17 a Kaduna, 16 a Yankin Babban Birnin Tarayya, 10 a Katsina, takwas a Sakkwato, bakwai a Edo, shida a Borno.
Sai kuma jihohin Yobe, da Ebonyi, da Adamawa masu mutum guda ko wacce.
Hukumar ta NCDC ta kara da cewa daaga cikin adadin wadanda suka kamu an sallami mutum 307 bayan sun samu sauki, yayin da mutum 51 suka riga mu gidan gaskiya.