Coronavirus: Kungiyar Izala ta sanar da janye Sallar Juma’a a Legas
Kungiyar Izalatul bidi’a wa Ikamatus Sunnah ta bada sanarwar janye sallar Juma’a a daukacin masallatanta a jihar Legas. Shugaban kungiyar na Legas Shaikh Sulaiman Ibrahim, ya shaidawa Aminiya cewa sun bada umarni ga daukacin masallatan kungiyar da ke Legas domin bin umarnin gwamnatin jihar na kare yaduwar cutar coronavirus. ” Tuni muka sanarwa daukacin masallatanmu […]
Kungiyar Izalatul bidi’a wa Ikamatus Sunnah ta bada sanarwar janye sallar Juma’a a daukacin masallatanta a jihar Legas.
Shugaban kungiyar na Legas Shaikh Sulaiman Ibrahim, ya shaidawa Aminiya cewa sun bada umarni ga daukacin masallatan kungiyar da ke Legas domin bin umarnin gwamnatin jihar na kare yaduwar cutar coronavirus.
” Tuni muka sanarwa daukacin masallatanmu saboda haka muma a nan masallacin mu da da ke limanci na 1004 a Victoria Island sallar Azahar za mu yi, kuma ba za mu yarda a haura mutum 50, idan muka ga an haura hakan sai mu bada umarni wasu su dakata har wasu su idar ko kuma suyi a gida.” in ji shi.
A ranar Laraba ne gwamnatin Legas ta bada umarnin hana taron da ya wuce na mutum 50 a masallatai ko coci-coci domin hana yaduwar cutar coronavirus.
A bangaren masallatan da ke karkashin jagorancin ‘yan darika da fari basu bada tabbacin ko zasu dakatar da sallar Juma’ar ba ko a’a bisa dalilin cewa, gwamnatin jihar bata sanarwa masarautar da ke jagoranta ‘yan Arewa ba.
Aminiya ta zanta da mai magana da yawun Masarautar Agege Alhaji Ali Na’ibi, wanda ya shaida cewa gwamnatin Legas bata sanar wa Masarautar Agege a rubuce ba, dan haka Masarautar bata da ikon hana mutane yin sallar Juma’a gobe idan sun fito.
” Ba mu da ikon sanarwa jama’a kada su fito sallar Juma’a gobe domin ba a sanar damu ba a hukumance, sannan idan mutane basu fito ba, ba mu da ikon fada masu su fito”
Sai dai daga baya mai magana da yawun Masarautar Agege Alhaji Ali Na’ibi ya kira wakilin Aminiya ta wayar salula ya ce wakilan gwamnatin Legas sun tuntubi Masarautar Agege da daren yau, dan haka idan gari ya waye da safiyar juma’a fadar Agege zata bada umarnin rufe daukacin masallatan Juma’a domin bin umarnin gwamnatin.
Haka zalika wani jigo a fadar Masarautar Agege Alhaji Ali Abubakar Danmajen Agege, ya shaida wa Aminiya cewa Masarautar Agege zata umarci daukacin limaman jihar da kada suyi sallar juma’a kowa ya yi a gida, domin ana samun mutum fiye da 100 a lokacin jam’in sallar juma’a.