Coronavirus: Ma’aikatan lafiya 29 sun kamu, an rufe asibiti a Filato

Gwamnatin jihar Filato ta rufe wani asibiti bayan ma’aikatansa 17 su kamu da cutar coronavirus, lamarin da ya sa jami’an lafiya da suka kamu da cutar a jihar kaiwa 29. Kwamishinan Lafiya na Jihar Filato, Dokta Nimkong Lar,  hakan ta faru ne bayan ce an gano cewa wasu marasa lafiya biyu da aka kwantar a […]

Coronavirus: Ma’aikatan lafiya 29 sun kamu, an rufe asibiti a Filato

Wani Sashe a wata cibiyar killace masu jinyar cutar coronavirus a Legas

Gwamnatin jihar Filato ta rufe wani asibiti bayan ma’aikatansa 17 su kamu da cutar coronavirus, lamarin da ya sa jami’an lafiya da suka kamu da cutar a jihar kaiwa 29.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Filato, Dokta Nimkong Lar,  hakan ta faru ne bayan ce an gano cewa wasu marasa lafiya biyu da aka kwantar a asibitin mai zaman kansa na dauke da cutar coronavirus.

Sakamakon haka ne aka tattance wadanda suka yi mu’ama’ala da marasa lafiyan a asibitin da ke yankin Rayfield a Karamar Hukumar Jos ta Kudu.

“Tantancewar ta nuna 17 daga cikin ma’aikatan lafiyan da suka yi mu’amala da marasa lafiyar sun kamu.

“Nan take Ma’aikatar Lafiya ta fara ba su kulawa, sai dai abin takaicin shi ne mutum daya daga cikinsu ya rasa ransa”, inji shi.

Ya kara da cewa zuwa ranar Laraba 17 ga watan Yuni jami’an lafiya 29 ne suka kamu da cutar a jihar Filato.

Kwamishinan ya yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, kada kuma su tsorata, amma su ci gaba da bin ka’idojin kariyar cutar da gwamnati ta ayyana domin kiyaye yaduwar ta.