Coronavirus: Majinyata biyu sun shiga buya a Borno

Mahukunta a jihar Borno sun yi kira ga mazauna birnin Maiduguri da su yi hattara kasancewar mutum biyu da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus sun shiga wasan buya da hukumomin lafiya. Kwamshinan lafiya na jihar, wanda kuma shi ne sakataren Kwamitin Kar-ta-kwana a Kan Yaki da Coronavirus, Dokta Salisu Kwaya-Bura, ya ce mutanen […]

Coronavirus: Majinyata biyu sun shiga buya a Borno

Gwamna Babagana Zulum

Mahukunta a jihar Borno sun yi kira ga mazauna birnin Maiduguri da su yi hattara kasancewar mutum biyu da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus sun shiga wasan buya da hukumomin lafiya.

Kwamshinan lafiya na jihar, wanda kuma shi ne sakataren Kwamitin Kar-ta-kwana a Kan Yaki da Coronavirus, Dokta Salisu Kwaya-Bura, ya ce mutanen biyu, namiji mai shekara 24 da mace mai shekara 42, sun shiga buya ne don kada a kai su inda ake killace masu dauke da cutar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa da yake karin bayani a kan halin da ake ciki a yakin da ake yi da COVID-19 a jihar da maraicen Lahadi, kwamishinan ya kuma ce an tura wasu jami’ai su gano inda mutanen suke, su kuma tafi da su wurin killace majinyatan.

“Da farko namijin ya amsa wayar jami’an bayan an debi kwayoyin halittarsa don a yi gwaji, amma sai ya kashe waya bayan an shaida masa cewa yana dauke da cutar.

“Idan aka debi kwayoyin halittar wadanda suka yi mu’amala da mutum na farko da ya kamu, da ma akan ba su shawara ne su killace kansu.

“Sannan kuma akan karbi lambar wayarsu domin a tuntube su idan sakamakon gwajin ya fito. Wadannan su ne matakan da ake bi bisa ka’idar hukumomin lafiya.

“Ba zai yiwu ka killace wanda ake zargin ya kamu ba. Ba mu da hurumin yin haka. Sauran mutanen da aka yiwa gwaji ma an kyale su sun tafi, amma da aka tabbatar sun kamu sun dawo cibiyoyin killace majinyata; yanzu muna da mutum 19 a cibiyoyi biyu.

“Amma shi wannan matashin ya zabi ya buya”, inji kwamishinan.

Dokta Kwaya-Bura ya kuma yi kira ga wadanda aka tabbatar sun kamu su daina dauka tamkar hukuncin kisa aka yanke musu, tun da galibin majinyata na warkewa.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu