Coronavirus: Majinyata sun yi zanga-zanga a Gombe
Fiye da mutum 20 da aka killace a Asibitin Cututtuka Masu Yaduwa da ke garin Kwadom na karamar hukumar Yamaltu Deba a jihar Gombe sun yi zanga-zanga suna karyata cewa suna dauke da cutar. Majinyatan sun yi zanga-zangar ne da taimakon mutanen garin, wadanda suka tare hanya. A lokacin da wakilinmu ya ziyarci garin, ya […]
Fiye da mutum 20 da aka killace a Asibitin Cututtuka Masu Yaduwa da ke garin Kwadom na karamar hukumar Yamaltu Deba a jihar Gombe sun yi zanga-zanga suna karyata cewa suna dauke da cutar.
Majinyatan sun yi zanga-zangar ne da taimakon mutanen garin, wadanda suka tare hanya.
A lokacin da wakilinmu ya ziyarci garin, ya ga yadda mutane ke cakuduwa da mutanen da aka killace.
Zanga-zangar dai ta dauki fiye da sa’oi biyu ana yi, amma har ’yan jaridar da suka je suka bar wajen babu wani jami’an tsaro ko wani jami’i daga ma’aikatar lafiya da ya ziyarci wajen.
- COVID-19: Majalisa ta shawarci gwamnatin Gombe ta rufe jihar
- COVID-19: Gwamnatin Gombe ta dakatar da sallar jam’i
Wasu daga cikin ‘majinyatan’ da ke killace a asibitin sun yi magana daga bayan shingen asibitin suna cewa su ba sa dauke da cutar, neman kudi kawai ake yi da su; don haka sun gaji a bar su su tafi gidajen su.
Wani ma’aikacin jinyar da ke kula da majinyatan wanda bai yarda a ambaci sunan shi ba ya ce masu dauke da cutar sun yi zanga-zangar ne saboda wasu daga cikin su sun yi korafin cewa akwai wata mata a cikin su tana da rauni a jikin ta ba a yi mata magani ba, amma ba don suna karyata cutar ba.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dokta Ahmed Muhammad Gana, a wata hira ta waya da manema labarai, ya bayyana cewa majinyatan sun gaji da zaman ne kawai shi ya sa suka yi wannan boren ba wai don babu cutar ba,