Coronavirus: Majinyatan Jigawa sun kai 116 bayan samun karin 33
An samu karin mutum 33 da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Jigawa, lamarin da ya kawo jimillar majinyatan jihar 116. Shugaban kwamitin yaki da COVID-19 kuma kwamishinan lafiya na jihar, Dokta Abba Umar Zakari, wanda ya fadi hakan, ya kara da cewa ana kokarin gano mutanen da suka yi mu’amala da sabbin […]
An samu karin mutum 33 da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Jigawa, lamarin da ya kawo jimillar majinyatan jihar 116.
Shugaban kwamitin yaki da COVID-19 kuma kwamishinan lafiya na jihar, Dokta Abba Umar Zakari, wanda ya fadi hakan, ya kara da cewa ana kokarin gano mutanen da suka yi mu’amala da sabbin kamun.
Dokta Zakari ya kara da cewa daga cikin mutum 33 na baya-bayan nan, 16 almajirai ne wadanda tuni suke cibiyar killace masu dauke da COVID-19 da ke hedikwatar jihar tun lokacin da jihar Kano ta dawo da su kimanin mako uku ke nan.
Ya ci gaba da cewa daga cikin mutum 116 da suka kamu jimilla, sittin almajirai ne yayin da sauran mutum 56 kuma galibi wadanda suka yi mu’amula ne da wadanda suke dauke da cutar.
Dokta Zakari ya kara da cewa shirye-shirye sun yi nisa na samar da cibiyar bincike a Jigawa domin yin gwaji a jihar maimakon kai samfuri Kano ko Abuja.
A halin da ake ciki kuma an kafa dokar hana fita a karamar hukumar Ringim bayan da aka samu mutum 29 dauke da cutar a yankin.
Jihar ta Jigawa dai na killace da almajirai sama da 30,000 wadanda aka mayar da su gida daga sassan Najeriya daban-daban.