Coronavirus: Majinyatan Kano ba su da alaka da juna

Karin mutum biyu da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Kano ba su da alaka da mutum na farko. Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa mutanen biyu sabbin kamuwa da cutar ba su yi wata mu’amala da mut una farko ba. Sai dai yayin da aka ce mutum na farko […]

Coronavirus: Majinyatan Kano ba su da alaka da juna

Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano

Karin mutum biyu da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Kano ba su da alaka da mutum na farko.

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa mutanen biyu sabbin kamuwa da cutar ba su yi wata mu’amala da mut una farko ba.

Sai dai yayin da aka ce mutum na farko ya yi tafiye-tafiye zuwa Legas da Abuja da Kaduna, inda mai yiwuwa ya kamu da cutar, babu cikakken bayani a kan yadda mutum biyun suka kamu.

A daren Litinin ne dai Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta tabbatar da samun karin mutane biyun bayan da sakamakon gwajin da aka yi musu ya nuna cewa suna da ita.

Tuni dai aka killace mutanen tare da wasu daga cikin mutanen da suka yi mu’amala da su wadanda suka hada da makusantansu da kuma abokan arziki a daya daga cikin cibiyoyin da aka tanada don killace wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar.

Sassauta dokar daukar fasinja

A halin da akae ciki kuma, gwamnatin jihar ta Kano ta sassauta dokar kayyade fasinjoji a motocin haya a fadin jihar.

Shugaban Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) Honorabil Baffa Babba Danagundi ya bayyana cewa gwamnatin ta sassauta dokar ne bayan sake nazarin da ta yi yayin wani zama da Kwamishinan Sufuri na Jihar Barista Muhammad Lawan da sauran masu ruwa da tsaki.

A cewar Danagundi, daga yanzu za a dauki fasinjoji biyu a keke mai kafa uku yayin da za a dauki mutum uku a tasi, mutum biyar kuma a motocin bas.

“Su ma motocin daukar kaya dokar ba ta bar su ba domin daga yanzu mutum daya za su dauka a gaban mota”. Inji shi.

Har ila yau Shugaban na KAROTA ya ce dole direbobin su samar da amawali ko takunkumi da man goge hannu a cikin motocinsu don kare kansu daga daukar cutar ta coronavirus.

Honorabil Danagundi ya yi kira ga direbobin da su girmama dokar domin duk wanda aka kama yana karya ta zai dandana kudarsa.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno