Coronavirus: MOPPAN ta dakatar da harkokin fim
Kungiyar ’yan fim ta Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN) ta umarci dukkan kungiyoyi da shugabannin masana’antar fim da ke Arewa da su dakatar da gudanar da fina-finai saboda cutar coronavirus. Wannan umarnin yana dauke ne a wata takarda da Sakataren Watsa Labarai na kungiyar na kasa, Malam Al’amin Ciroma ya sanya wa hannu, […]
Kungiyar ’yan fim ta Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN) ta umarci dukkan kungiyoyi da shugabannin masana’antar fim da ke Arewa da su dakatar da gudanar da fina-finai saboda cutar coronavirus.
Wannan umarnin yana dauke ne a wata takarda da Sakataren Watsa Labarai na kungiyar na kasa, Malam Al’amin Ciroma ya sanya wa hannu, inda takardar ta nuna cewa an dauki wannan matakin ne domin kiyaye yaduwar cutar.
A cewar takardar, “ganin yadda annobar cutar Covid-19 ke yaduwa a wasu jihohin Najeriya da Babban Birnin Tarayya Abuja, shugabannin Kungiyar MOPPAN ta dakatar da dukkanin harkokin fina-finan Hausa ta Kannywood. Wannan sanarwar za ta yi aiki ne na kwana 30 daga wannan lokaci.
“Shugaban kungiyar ya nemi dukkan qungiyoyin Kannywood da su bi umarnin, ta hanyar dakatar da dukkan harkoki da suka shafi fim a jihohinsu, wanda zai taimaka wajen wayar da kan al’umma a yunqurin daqile yawaitar cutar.”
Da Aminiya ta tuntubi Shugaban MOPPAN na kasa, Dr. Ahmad Muhammad Sarari domin tabbatar da sahihancin takardar, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce, “lallai takardar daga mu take. Mu muka bukaci dakatarwar.”
Ita dai wannan sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke cikin ruxani kan cutar ta kurona.